A yayin da Mabiya addinin Kirista ke cigaba da shirye-shiryen shan shagulgulan Kirsimeti da sabuwar shekara, wata mata Musulma, Hajiya Ramatu Tijjani, ta raba wa Kiristoci marayu da matan da majajensu suka rasu kayan abunci da atamfofi da nufin nuna musu zaman tare.
Jahar Kaduna dai na cikin Jahoshin Arewa maso yammacin Najeriya da ke da mabiya addinai daban-daban wadanda ke zama tare, shi yasa a duk lokacin da wani sha'ani ya tashi akan sami mabiya daban-daban a wuri guda saboda zaman tare. Hajiya Ramatu Tijjani, na cikin mata Musulmi da kan tallafa wa Kirista idan lokutan bukin Kirsimeti da sabuwar shekara sun zo. Kuma ta ce tsadar kayan abunci ya sa ta sayi buhunan shinkafa don tallafa wa Kirista a Kaduna.
Hajiya Ramatu ta ce duk da yake ba tun yanzu ta fara nuna wa mabiya addinin Kirista zaman tare ba, amma tsadar abun a wannan shekara ya sa ta maida hankali kan abunci kuma ta samu natsuwa saboda tabbatar wa da Kiristoci a na tare.
Malamin Cocin da Hajiya Ramatu Tijjani ta raba ma wannan tallafi, Pastor Yohanna Buru ya ce irin wannan taimako na nuna jinkai da tausayi kuma zai taimaka wajen kara hada kawunan Musulmi da Kirista a Najeriya baki daya.
Pastor Buru ya ce taimaka wa marayu da mata zawarawa sai mai tausayi da jinkai saboda haka ya yi wa Hajiya Ramatu Tijjani godiya saboda tallafa wa Kirista ba tare da la'akari da banbancin addini ba.
A baya can dai jahar Kaduna ta yi kaurin suna wajen rikice-rikicen addini, wanda ya sabbaba zaman doya da manja tsakanin mabiya, sai dai yanzu abubuwan sun sauya zuwa zaman lafiya da fahimtar juna.
Saurari cikkken rahoton Isah Lawan Ikara: