KADUNA, NIGERIA - Dama dai tun farko Jam'iyyar PDP ta koka game da rashin amince mata da yin taron a filin wasa na Ahmadu Bello da ta nema da farko, sai kuma ga shi taron ya yi karo da fushin wasu matasa.
Kafin matasan su afkawa taron dai ‘dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar ta PDP Alhaji Atiku Abubakar ya sha alwashin magance matsalolin Najeriya.
Atiku ya yi rantsuwa cewa idan aka zabe shi zai magance matsalar tsaro, rashin aikin yi, kuma zai gyara hanyoyin da su ka lalace masamman tsakanin Kaduna zuwa Jos da kuma Kaduna zuwa Kano da ba a gama ba.
Shugaban Jam'iyyar PDP na kasa Mr. Iyorchia Ayu ma ya ce Jam'iyyar shi ce ta san lalurar 'yan Najeriya kuma ta na da magani.
Ayu ya ce 'yan Najeriya ba za su iya ci gaba da zama cikin zullumin matsalar tsaro ba saboda akwai bukatar sauyi don kawo wanda zai magance matsalolin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki.
Game da harin da ya kusa tashin taron na Jam'iyyar PDP a Jihar Kaduna, magatakardan Jam'iyyar a Kaduna, Alhaji Ibrahim Aliyu Wusono ne ya yi bayani kan abun da ya faru.
Yakin neman zaben Jam'iyyar PDP dai ya zo daidai da ranar da wasu kungiyoyi shida na Arewa su ka gayyaci 'yan-takarar shugaban kasa na Jam'iyyun APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu da na LP, Mr. Peter Obi, dalilin da ya sa garin Kadunan ya chunkushe har wasu guraren mutane su ka dunga tafiya a kas.
Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara: