KADUNA, NIGERIA - Da ya ke Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na Jam'iyyar NNPP, wanda ya kamata ya fara jawabi, ya aike da tadardar cewa ba zai halarci taron ba, Sanata Bola Ahmed Tinubu na APC ne ya fara jawabi, inda ya yi alkawarin magance matsalolin tsaro, tattalin arziki da ilimi wadanda ya ce su na daga cikin manyan matsalolin Arewa.
Kuma da ya ke gwamonin arewa 7 ne su ka rako shi, Shugaban Kungiyar Gwamonin APC, Alhaji Atiku Abubakar Bagudu, ya ce Sanata Bola Tinubu bashi ya ke bin Arewacin Najeriya. Ya na mai nuni da yadda Tinubun, a cewarsa, ya yi ta goyon bayan 'yan takarar arewacin Najeriya a baya, tun ma bai fara sha'awar wani mukamin siyasa ba.
Shi kuwa Mr. Peter Obi na Labour cewa ya yi Najeriya ta riga ta durkushe saboda babu tsaro, ba tattalin arziki da dai sauran matsaloli- sannan ya yi alkawarin ceto kasar idan ya ci zabe.
Cikin 'yan takara shidan farko da kungiyoyin arewan su ka gayyata dai biyar sun halarta kuma kungiyoyin sun ce za su duba yuwuwar gayyatar sauran 'yan-takarar don bai wa 'yan kasa zabi cikin masu neman zama shugaban Kasa.
Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara: