Hauhawar farashin kayan masarufi da tsadar rayuwa dai ya sa cin abincin sau uku a rana, ya fara gagara a wasu gidaje yayin da wasu 'yan-kasuwa ke rufe shagunan su saboda farashin kayan ya fi karfin jarinsu.
Saboda haka ne Majalissar Limamai da Malamai ta jihar Kaduna ta kira taron manema labaru don nunawa gwamnati hadarin da ke fuskantar kasar baki daya.
Na'ibin Limamin Masallacin Juma'a na Tudun-Wada 'Yan-lilo, Sheik Idris Mohammed Sabon-gari, shi ya yi bayani ga manema labarai a madadin majalissar, inda ya nuna da cewa idan aka bari talakawa su ka tunzura to abun ba zai yiwa kowa kyau ba.
Haka nan kuma Majalissar ta alakanta matsalar tsadar rayuwar da ake ciki da kuma matsalar tsaro, kamar dai yadda limamin Masallacin Juma'a na Al-Adamawy Kaduna, Imam Aminu Umdah ya nuna da cewa idan da a ce akwai tsaro to kowa zai koma gona don noma abun da zai ci amma rashin tsaron ya hana.
Majalissar ta ce mafita game da tsadar rayuwar da jefa rayuwar talaka cikin kunci kawai ita ce kowa ya koma ga Allah sannan gwamnati da masu kudi su taimaki al’umma.
Har yanzu dai damina bata wuce wata uku da karewa ba kuma kafin ganin wani sabon kayan abincin noman damina sai kusan watanni shida nan gaba, abun da yasa wasu ke ganin idan ba a dauki mataki ba to komai ma na iya faruwa a wannan Kasa.
Ga cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:
Dandalin Mu Tattauna