Shugaban kungiyar 'yan-kasuwar Katako a Pantekan Alh. Ahmed Mohammed Dan-Asabe ya tabbatarwa Muryar Amurka afkuwar wannan iftila'in gobara kuma ya ce akwai wata mota da ke cike da katako wadda ita ma ta kone kurmus.
Ya ce da misalin karfe dayan daren Talata zuwa asuban Laraban nan ne wutar ta tashi, sai dai bata yi barna kamar ta bara ba kuma ba a rasa ran ko da mutum daya ba.
Shekara biyar kenan a jere ana irin wannan gobara a bangaren masu sayar da katako na Kasuwar Panteka tsohowa inda ake asarar dukiya mai yawan gaske.
Shugaban kungiyar masu sayar da katakon Alh. Ahmed Mohammed ya ce ba a gano musabbabin tashin gobarar ba kuma har yanzu ba gama kididdige kimar dukiyar da aka yi asara ba.
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna, Mr. Paul Aboi ya tabbatar da wannan gobara kuma ya ce cikin daren ne hukumar shi ta kai daukin da aka kashe gobarar shi yasa ba ta cinye rumfunan wasu masu sayar da katakon ba.
Dandalin Mu Tattauna