Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dattawan Najeriya Sun Sadaukar Da Albashinsu Ga Iyalan Wadanda Harin Bom Ya Shafa A Kaduna


Ziyarar Da 'Yan Majalisar Dattijan Najeriya Suka Kai Wa Wadanda Harin Bom Ya Shafa A Garin Tudun Biri Da Ke Karamar Hukumar Igabi, Kaduna
Ziyarar Da 'Yan Majalisar Dattijan Najeriya Suka Kai Wa Wadanda Harin Bom Ya Shafa A Garin Tudun Biri Da Ke Karamar Hukumar Igabi, Kaduna

Dukkan ‘yan majalisar dattawa 109 na Najeriya sun ce sun sadaukar da albashin su na wannan watan Disamba gaba daya ga iyalan wadanda su ka rasu sanadiyyar harin jirgin saman soji a garin Tudun Biri na jihar Kaduna.

Manyan jami'an gwamnati da shugabanni daga sassa daban-daban na Najeriya na ci gaba da nuna damuwa tare da tabbatar da cewa za’a yi bincike kan harin jirgin saman sojan da ya kashe mutane sama da tamanin a garin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Mako guda ke nan tun bayan da ibtila'in harin jirgin saman soja mara matukin da ya hallaka masu taron mauludi a garin Tudun Biri, amma har yanzu ana ci gaba da ganin jagorori daga bangarori daban-daban su na ci gaba da ziyarar nuna alhini.

Ko a ranar Lahadi ma sai da tawagar 'yan-majalisar dattawa ta shiga garin na Kaduna domin ta'aziyya da jaje.

Mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Ibrahim Jibrin, ya ce majalisar dattawan Najeriya ta gamsu cewa, wadanda harin bom din ya jikkata suna samun sauki kuma an sami ci gaba da wuri mai tsafta kuma ana ba da magani kamar yadda ya kamata.

Sanata Barau ya ce ‘yan majalisar dattijai su 109 sun sadaukar da albashin su na wannan watan Disamba gaba daya ga iyalan wadanda su ka rasu sanadin harin jirgin na Kaduna.

Shugaban Kwamitin Sadarwa na majalisar dattijan, Sanata Ikra Aliyu Bilbis, ya ce majalisar za ta tabbatar da ta yi binciken kwakwab kan lamarin.

Basaraken yankin, Malam Magaji Aliyu Adamu, ya bayyana irin tashin hankalin da al’ummar yankin su ka gani, inda ya ce wasu masu babura da su ka kawo dauki, don daukar wadanda bom din ya jikkata, bom na biyu a kan su ya fada, inda ya yi dai-dai da naman su.

Kafin zuwan tawagar majalisar dattawan a Kaduna ma sai da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribado, ya jagoranci manyan jami'an gwamnati da na tsaro, inda ya sha alwashin yi wa tufkar hanci kan irin wannan ibtila'i baki daya.

Da ya ke wasu na ta nuna fargabar cewa, wannan batu zai iya wucewa ba tare da gwamnati ta dauki wani mataki ba, gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya ce ai sun riga sun yi rantsuwa kan kare rayukan mutane.

Har kawo yanzu ba'a bayyana sunayen wadanda za su yi binciken da ake ta alkawarin yi don bankado gaskiyar ainihin abun da ya faru ba, duk kuwa da cewa gwamnati ta yi alwashin yin binciken cikin gaggawa.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:10 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG