Matasa daga sassa daban-daban ne su ka zagaya a sassan birnin Zariya don bayyana damuwa game da harin jirgin sojan Najeriya da ya yi sanadin rasuwar mahalarta taron Mauludi da dama a garin Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabin jihar Kaduna.
Wannan zanga-zangar ta tike a sakatariyar Karamar Hukumar Zariya, inda daya daga cikin jagororin zanga-zangar ya bayyana damuwar su, yana mai cewa ba za su lamincewa kisan kiyashi daga 'yan bindigar daji ba,a daya bangaren kuma daga rundunar tsaron kasa da sunan kuskure.
Mataimakin shugaban karamar hukumar Zariya, Alhaji Idris Yusuf Idris, shi ne ya saurari koken matasan kuma ya tausasa su da cewa za’a tabbatar da daukar matakin da ya dace kan lamarin.
Idris ya ce wannan abu ya bata musu rai, ya tayar musu da hanakali kuma sun yi tir da shi.
Kwamared Muttaka Maiwada Goga, shugaban daya daga cikin kungiyoyin da su ka yi wannan zanga-zanga ne, kuma ya ce akwai sauran magana saboda a cewar shi wannan zanga-zanga ba za ta tsaya ba har sai mahukunta sun dauki mataki.
Shi ma da ya ke tsohon dan-gwagwarmaya ne, tsohon Dan-Majalisar Dattawan shiyya ta biyu da ke jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani ya ce matukar ba'a yi wa tufkar hanci kan irin wannan ibtila'i ba, to matsala ba za ta kare ba.
Sanata Sani ya ce “Saboda haka a ganin na sun yi sakaci, sun yi gangagnaci kuma dole ne a dauki mataki akan irin wadannan abubuwa da suke faruwa. Idan ba’a tashi tsaye akan irin wadannan abubuwan ba to hakan zai ci gaba da faruwa.”
A ranar Alhamis ake sa ran gwamna jihar Kaduna Uba Sani zai dawo daga tafiya don takakkiya zuwa garin Tudun Biri tare Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shatima.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna