Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cika Kwanaki Arba’ın Da Kai Hari Tudun Biri


'Yan Bindiga sun kai hari
'Yan Bindiga sun kai hari

Sama da kwanaki arba'in da harin jirgin sojan da su ka ce kuskure ne a garin Tudun Biri, wasu al’ummar yankin sun ce har yanzu gwamnati ba ta cika musu alkawurran da ta dauka ba. 

KADUNA, NIGERIA - Muryar Amurka ta samu duba halin da al’ummar Tudun Birin ke ciki bayan kammala addu'ar kwana 40 da kai harin jirgin sojan Najeriya a garin.

'Yan uwa da abokan arzikin wadanda harin bom din ya hallaka da dama ne dai su ka halarci taron addu'ar arba'in da aka yi a garin na Tudun Biri.

Sai dai duk da kukan jinkirin cika alkawurran gwamnatin, jagororin al’ummar Tudun Birin sun ce gwamnati na kokari. Manyan garin sun ce bayan share hanyar garin yanzu haka an haka tushen fara ginin asibiti a garin.

Dama dai tun farkon harin, masana harkon tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai-ritaya suka nuna yuwar cewa za a yi biris da daukar mataki a bangaren gwamnati kuma ya ce gashi dai yanzu bayan kwanaki arba'in ba wani abu ba ya canja.

Babban abun da aka fi sa ran al’ummar Tudun Biri za su samu cikin gaggawa shine tallafin kudin da aka tattara, to sai dai dama tun lokacin kaddamar da kwamiti kan harin, gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ce wasu alkawurran kudaden sai an bi sahun su.

Daya daga cikin abubuwan lura dai shine daukewar kafar jami'an da daina ganin baki a yankin da masana ke cewa,akwai bukatar zuba jami'an tsaro a yankin baki daya.

Saurari cikakken shirin daga Isah Lawal Ikara:

Kwana Arba’ın Bayan Harin Da Aka Kai Tudun Biri.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:22 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG