Shirin Manuniya na wannan mako ya maida hankali ne akan halin da siyasar Najeriya ke ciki tun bayan sanar da komawar tsohon gwamnan jahar Kaduna, Nasiru El-rufa'i jam'iyyar SDP.
Shirin Manuniya na wannan makon ya duba batutuwan da suka shafi rikicin cikin gida na jam'iyyu siyasa a Najeriya da Ghana sai kuma hirar Gwamnan jihar Katsina.
Majalisar wakilan Najeriya ta ce hauhawar shaye-shayen miyagun kwayoyi da cin zarafin da ke faruwa a gidaje babbar barazana ce da ka iya durkusar da Najeriya idan masu ruwa da tsaki ba su hada karfi da karfe ba.
Bude babbar kasuwar shanu ta Birnin Gwari na cikin manyan sharuddan sulhun da aka yi da 'yan-bindiga kuma shugabannin kasuwar sun ce an cika wannan sharadi.
Duk da barazar bakawa gonakin wasu manoma wuta da 'yan-bindiga su ka yi a wasu yankunan Birnin Gwari makonni biyu da su ka gabata, sulhun da gwamnatin jahar Kaduna ta assasa ya fara aiki.
Shirin Manuniya na wannan mako ya maida hankali ne akan maganar shugabanci da tsaro a Najeriya sai kuma shirye-shiryen Zaben shugaban kasar Amurka.
Domin Kari