Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sulhu Tsakanin 'Yan Bindiga da Gwamnatin Kaduna Ya Fara Haifar Da 'Da Mai Ido


Kasuwa
Kasuwa

Bude babbar kasuwar shanu ta Birnin Gwari na cikin manyan sharuddan sulhun da aka yi da 'yan-bindiga kuma shugabannin kasuwar sun ce an cika wannan sharadi.

Kasa da watanni biyu da gwamnatin Jihar Kaduna ta jagoranci sulhu tsakanin ta da 'yan-bindiga a yankin Birnin Gwari a jahar Kaduna, al-umomi a yankin sun fara farin cikin samun walwala ta hanyar bude kasuwanni da hanyoyin da sa baya suka gagara, yayain da wasu suke kokawa.

Bayan kauracewa babbar kasuwar shanu ta Birnin Gwari kimanin tsawon shekaru 10, yanzu kasuwar na cika da Fulani da Hausawa ba tare da kyarar juna ba, sakamakon sulhu tsakanin al-umomin yankin birnin Gwari da kuma 'yan-bindiga wanda gwamnati ta shiga tsakani.

Wakilin Muryar Amurka a jihar Kaduna, Isah Lawal Ikara, ya wanki kafa har zuwa Kasuwar ta birnin Gwarin wanda aka fi sani da Kara.

Ya ce ya hadu da wasu tubabbun 'yan-bindigan da suka yi na'am da wannan sulhun, sannan ya nemi jin ta bakin su a game da yaushe rabon su da shigowa cikin gari ko kasuwa. Muhammad Bello daya ne daga tubabun 'yan bindiga, wanda ya sheda ma wakilin Muryar Amurka cewa "yana cike da farin cikin da bai taba ji a rayuwar shi ba tun da suka tashi, Da Fulani da Hausa yau gashi mun hadu cikin farin ciki.

"An zauna anyi sulhu da Fulani, da Hausawa da hukuma da mutanen daji, an zauna ance mu zauna lafiya kuma kowa ya yarda ya dauki amana, sannan ya kara da cewa baya fargabar cewa wannan karon hannun agogo zai koma baya".

Sauran tubabun 'yan bindigan da Isah ya tattauna da su suma sun ce sun kwashe sama da shekaru goma basu shigo kasuwa ko cikin gari ba amma yanzu suna walwala. Da ya bukaci ya ji yaushe zasu dawo da bindigogi tun da zaman lafiya ta samu, sun ce zasu dawo da bindigogin su idan komai ya ci gaba da tafiya kamar yanzu ba da jimawa ba.

Bude babbar kasuwar shanu ta Birnin Gwari na cikin manyan sharuddan sulhun da aka yi da 'yan-bindiga kuma shugabannin kasuwar sun ce an cika wannan sharadi.

A latsa nan domin sauraron rahoton Isah Lawal Ikara:

A SPECIAL REPORT ON BIRNIN GWARI DIALOGUE.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:21 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG