Hukumar ba da agajin gaggawa a Najeriya, NEMA, ta fara kai kayayyakin tallafi ga wadanda rikicin makiyaya da 'yan Bachama ya shafa a jihar Adamawa.
Yanzu haka dai an soma samun martani da cece-kuce game da ficewar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, yayi akan ficewa daga jam'iyya mai mulki ta APC.
Gwamnatin jihar Adamawa ta dauki nauyin jinyar yara da matan Fulani makiyaya da aka raunata yayin wani hari da aka kai musu a rugagensu dake wasu kauyukan karamar hukumar Numan, da ‘yan kabilar Bachama ke da rinjaye .
Babban kotun jihar Adamawa ta dakatar da sassan biyu daga duk wani kuduri game da wannan batu, har sai an kammala sharia.
Hukumar NEMA tace dama tana cikin shirin ko ta kwana saboda mutane masu rauni kamar mata, yara da tsofaffi
Yanzu haka wata sabuwar dambarwa ta sake barkewa a jam’iyar APC reshen jihar Taraba a tsakanin bangarori biyu na shugabanin jam’iyar da ke da alaka da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ‘yan bangaren ‘yan Integrity dake tare da shugaba Buhari.
A dai-dai lokacin da kwamitin da jam’iyyar APC ta kafa ke gudanar da taron jin ra’ayin jama’a game da batun sake fasali da zamantakewa da kuma siyasar Najeriya a fadin tarayyar kasa, wasu dattijai na ganin kasar ba zata rabu ba.
Yanzu haka dai an soma musayar kalamai a tsakanin yan jam’iyar PDP dake mulkin jihar Taraba, da kuma yan hadakar kungiyar siyasa ta Integrity a jihar game da rancen kudaden da gwamnatin jihar ke karba da kuma yadda gwamnan jihar a yanzu Darius Dickson Isiyaku, ke jagorantar jihar.
Yanzu haka yajin aiki da kananan likitocin Najeriya ke yi ya fara jefa majinyata cikin wani hali, sakamakon rashin samun kulawa lamarin da yakai cewa jami’an jinya ne kawai ke kula da marasa lafiyan.
An dauki tsauraran matakan tsaro a jihohin Adamawa da Taraba domin bukukuwan babar sallah.
Wani sabon rikici ya sake barkewa a jam’iyar APC reshen jihar Taraba yayin da tsohon mukaddashin gwamnan jihar Garba Umar UTC, ke sauya sheka zuwa jam’iyar.
Wannan ya biyo bayan matakin da kansilolin karamar hukumar hukumar suka dauka, sakamakon bincike da aka fara kan rikicin da ya halaka rayuka da dukiya mai yawa.
Gwamnatin jihar Taraba ta kaddamar da aikin hanyar zuwa Pantisawa da aka yi watsi da ita fiye da shekaru goma.
Hadakar kungiyar maharba masu aikin sa kai da yan kato da gora a jihar Adamawa, sunyi ikirarin cewa zasu ci gaba da taimakawa sojoji a yaki da Boko Haram muddin za’a ci gaba da tallafa musu.
Kwamishinan yada labarai na jahar Ahmed Sajoh ne ya bayyana haka, lokacinda yake magana biyio bayan kisan Kwamanda Bukar Jimeta.
Rahotanni sun ce sama da mayakan Boko Haram 100 ne su ka yi wa garin Dagu da ke yankin Askira Uba kawanye, garin da ke kan iyakar jihar Adamawa da Borno, lamarin da ya haifar da artabu tsakanin mayakan da wasu maharba har ya kai ga mutuwar wani babban kwamandan maharban.
Yayin da dangantaka ke kara tsami a tsakanin bangaren majalisar dokoki da ta zartarwa, manazarta da kuma lauyoyi na ganin akwai bukatar karatun ta natsu a tsakanin bangarorin biyu kamar yadda yake a bisa tsarin demokaradiyya.
Allah ya yiwa tsohon gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai rasuwa.
Yayin da aka shiga kwana na uku a yajin aikin da mahauta da fataken dabbobi ke yi a jihar Taraba, ana fuskatar karancin nama da nono a fadin jihar. Gwamnatin jihar ta nuna bacin ranta da kuma cewa za a sasanta.
Domin Kari