Shugabanin jam’iyar APC a jihar Taraban dake tare dabangaren ministan harkokin mata Sen. Aisha Jummai Alhassan, ne dai suka soma jangwalota, inda suka bukaci tsohon shugaban jam’iyar wanda yanzu ya zama jakada, wato Ambassada Hassan Jika Ardo, da suka raba gari da ministar da ya hanzarta ya maido da mota kirar Jeep, wadda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya ba shi a watannin baya.
A wata wasika da suka aikawa tsohon shugaban jam’iyar ‘yan bangaren Aisha Jummai, na ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasan ne Atiku Abubakar ya bukaci a maido da motar, batun da ‘yan bangaren su Jika Ardon, wato ‘yan APC Integrity dake goyon bayan shugaba Buhari ke cewa ba zata sabu ba, wai bindiga a ruwa!.
A ganawarsu da manema labarai ‘yan APC Integrity sun yi tir da wannan batu, inda Alh. Iliyasu Mu’azu, ya ce ai ba’a taba yin kyauta a kwace ba.
To sai dai kuma a martanin su shugabanin jam’iyar APC a jihar sun musanta zargin cewa kwatar mota na da nasaba da dambarwar Buhari da Atiku. Alhaji Abdullahi Ade, wanda ke cikin shugabanin jam’iyar a jihar dake tare da bangaren ministar matan ya ce sun dau wannan mataki ne domin mayar da motar jam’iyar.
Da yake tsokaci game da wannan takaddamar tsohon shugaban jam’iyar APC, Ambassada Hassan Jika Ardo, ya ce shi kyauta aka bashi ba ta jam’iya ba ce.
Saurari rahoton Ibrahim Abdul'aziz daga Yola.
Facebook Forum