Gwamnatin jahar Taraba ta dakatar da shugaban karamar hukumar Sardaua John Yeb. Biyo bayan binciken da aka soma yi game da wadanda ke da hannu a rikicin tsaunin Mambilla, wanda ya jawo hasarar rayuka da dukiya.
Kungiyoyi da dama dai sun yi zargin cewa akwai hannun wasu yan siyasa a wannan rikici na Mambilla.
Kansilolin karamar hukumar Sardaunar ne suka gabatar da kudurin dakatar da shugaban karamar hukumar Mr John Yep,kuma ba tare da wani jinkiri ba gwamnatin jihar ta amince, har ma tuni aka rantsar da shugaban majalisar kansilolin karamar hukumar,Reverend Godwill Sol a matsayin shugaban riko.
To ko shin kwalliya zata biya kudin sabulu da dakatarwar? shugaban rikon Godwill Sol, yace wannan mataki zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a yankin.
To sai dai da alamun wannan dakatarwar tuni ta soma jawo cece-kuce,a jihar inda masana harkar sharia ke ganin akwai abun dubawa.
Barr. Idris Abdullahi Jalo na cikin shugabanin kungiyar lauyoyin jihar Taraba,yace kansiloli basu da hurumin dakatar da shugaban karamar hukumar, to amma suna da ikon tsigewa.
Ita kuwa a nata bangaren,Gwamnatin jihar tace zata ci gaba da nemo bakin zaren magance tashe tashen hankulan da ake samu a jihar, inda kwamishinan yada labaran jihar Anthony Danburam ke kira da ake kai zuciya nesa.
Facebook Forum