Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya, na cewa wani rikici mai nasaba da kabilanci da kuma rikicin gonaki ya barke a wasu kauyuka da ke kusa da garin Numan, lamarin da ya jawo asarar rayuka da dukiya.
Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Dong da Lawaru da Kedemure da wasu kauyuka da dama a karamar hukumar ta Numan da Demsa dake kudancin jihar Adamawa, wanda kuma kawo yanzu ba a tantance adadin rayukan da suka salwanta ba.
Har ya zuwa yanzu dai ba a bayyana maharan ba, sai dai kuma wannan na zuwa ne kasa da mako guda da kisan da aka yiwa wasu ‘yayan Fulani makiyaya da matansu a yankin na Numan da akasari al’ummar Bachama ne, wanda hakan ne yasa ake danganta lamarin da rikicin makiyaya da manoma.
Tuni dai har gwamnatin jihar Adamawan ta kira wani taron gaggawa na shugabanin tsaro a jihar don daukan mataki. Kwamared Ahmad Sajo, kwamishinan harkokin yada labarai a jihar ya yiwa manema labarai bayanin halin da ake ciki da kuma matakan da aka dauka.
Ya zuwa yanzu dai an kara tura ‘karin jami’an tsaro ciki har da sojoji, yayin da a wasu wuraren ake zaman dar-dar. SP Othman Abubakar kakakin rundunan yan sandan jihar Adamawa, ya tabbatar da kara tura jami’an tsaron.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum