Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Samun Cece-kuce Kan Ficewar Atiku Abubakar Jam'iyar APC


Yanzu haka dai an soma samun martani da cece-kuce game da ficewar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, yayi akan ficewa daga jam'iyya mai mulki ta APC.

A wata sanarwa da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya fitar tun da farko, ya ce ya bar jam'iyyar APC ne saboda gazawarta wajen cika alkawuran da ta daukarwa 'yan Najeriya, na kawo sauyin halin da kasar take ciki.

Da ya tuna baya, Atiku yace a shekarar 2013 haka nan suddan yana zaman-zamansa wasu jagororin jam'iyyar APC suka same shi da gayyatar ya shiga jam'iyyarsu bayan da aka samu rarrabuwar kai a tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP.

To sai dai a wani lamari na ba zata, duk da cewa Atiku bai bayyana jam’iyar da zai koma ba, kawo yanzu, kusoshin jam’iyar PDP a jihar Adamawa, jiharsa ta haihuwa ne suka tarbe shi a filin saukar jiragen sama na Yola, jim kadan da ficewarsa daga jam’iyar APC.

Barr. A.T Shehu shine shugaban jam’iyar PDP a jihar ya bayyana dalilansu na wannan tarba.

Sai dai kuma yayin da ‘yan PDP ke mika goron zawarcin tsohon mataimakin shugaban kasar, su kuwa ‘yan APC cewa suke Allah raka taki gona! A cewar sakataren jam’iyar a jihar Alh.Saidu Naira.

Yanzu dai an zura ido aga makomar ‘ya’yan gidan siyasar Atiku dake gwamnatin APC, ciki har da gwamnoni da ma ministoci akan shin zasu bi shine ko kuma a’a.

Domin karin bayani saurari rahoton Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG