Wadanda lamarin yafi shafa a yanzu sune majinyatan da basu da galihu na zuwa asibitocin kudi kamar yadda wasu majinyata a jihar Taraba arewa maso gabashin kasar suka koka.
Dakta Kefas Thomas, na daga cikin shugabanin kungiyar likitocin Najeriya a jihar Taraba, ya ce sun tsunduma wannan yajin aikin ne, biyo bayan shakulatin bangaro da suke zargin gwamnatin kasar na nuna musu na rashin biyansu hakkokinsu.
Da yake zantawa da manema labarai Dakta Thomsa, ya ce zasu ci gaba da yajin aikin har sai gwamnatin ta biya musu bukatunsu.
Suma dai shugabanin asibitoci sun koka da yajin aikin likitocin, Dakta Inusa Wuza, dake zama shugaban asibitin gwamnatin tarayya na FMC, Jalingo ya ce abin takaici ne, to amma suna kokarin lallabar likitocin.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum