Wannan farmaki na zuwa ne kwana biyu bayan mutuwar daya daga cikin kwamandojin dakarun Najeriyar Kanar Dahiru Bako, wanda ya rasa ransa a wani harin kwantan-bauna da mayakan Boko Haram suka kai akan sojojin Najeriya a ranar Lahadi.
“A cikin wannan farmaki da aka kai, an kashe wasu kwamandojin su ‘yan Boko Haram da ‘yan ISWAP wadanda suka hada da Abu Usman, Alhaji Shettima, Madu Mainok, Abubakar Gana, Abu Sumayya da kuma Amir Ta’am.” In ji Navy Commander Abdulsalam Sani na hedkwatar tsaron Najeriya.
Wata sanarwa da hedkwatar tsaron ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Juma'a ta kara tabbatar da wannan hari da aka kai.
“Dakarun saman Najeriya, karkashin Operation Lafiya Dole sun yi daidai da mabuyar mayakan Boko Haram tare da halaka mayakansu da dama.” Sanarwar mai dauke da sa hannun Kakakin hedkwatan tsaron ta Najeriya Manjo Janar John Enenche ta ce.
Farmakin wanda aka kai shi ta sama, ya wakana ne karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Operation Lafiya Dole a ranar Larabar 23 ga watan Satumbar 2020 wanda hedkwatar ta ce ya yi nasarar kawar da wasu manyan kwamandojin kungiyar ta Boko Hara/ISWAP.
Hedkwatan tsaron Najeriyar ta kara da cewa, an tsara farmakin ne bayan bayanan sirri da ta tattara wadanda suka nuna cewa akwai wasu gine-gine da “kwamandojin mayakan kungiyar 'yan ta’addan ta Boko Haram suka mayar mabuyarsu a yankin dajin Sambisa."
“Nan da nan aka ta da jiragen yakin sama wadanda suka yi raga-raga da wurin, inda har aka ga gine-gine sun kama da wuta.” In ji Eneche.
Wannan hari a cewar hedkwatar tsaron ta Najeriya, an kai shi ne yayin da aka kaddamar da wani sabon shirin wanzar da zaman lafiya mai taken “Hail Storm 2” da ke karkashin Shirin “Operation Lafiya Dole.”
Sai dai sanarwar ba ta fadi adadin mayakan da aka halaka ba amma hedkwatar taron ta Najeriya ta wallafa wani hoton bidiyon tauraron dan adam, wanda ya nuna yadda aka kai harin da kuma yadda mabuyar mayakan ta Boko Haram din ke cin wuta.
Saurarin karin bayani a wannan rahoto da Hassan Maina Kaina ya hada mana:
Facebook Forum