Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhawara Kan Batun Sauya Hafsoshin Sojin Najeriya


Shugaba Buhari na Najeriya tare da babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Tukur Buratai.
Shugaba Buhari na Najeriya tare da babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Tukur Buratai.

Tun bayan da ake samun karin haren-haren mayakan Boko Haram musamman wadanda suka rika kai wa akan gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Prof. Babanga Umara Zulum da wasu sassan kasar, muhawarar yin garanbawul ga fannin hafsoshin sojin kasar ta sake kunno kai.  

A ‘yan watannin da suka gabata n yi ta kiraye-kirayen neman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya sauya shugabannin hukumomin tsaron kasar, a lokacin da matsalar tsaro ta yi kamari a wasu sassan kasar.

Baya ga matsalar Boko Haram da aka kwashe shekara sama da 10 ana fama da ita, wani yanki da yake matukar fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga shi ne na arewa maso yammaci, musamman a jihohon Katsina, Zamfara da Sokoto.

Masu satar mutane da shanu sukan ci karensu ba babbaka a wadannan yankuna duk da cewa gwamnatin tarayya ta tura jami’an tsaro a yankunan domin kawar da maharan.

Rahotanni na nuni da cewa, lamarin ya dan lafa a ‘yan makonnin baya-bayan nan, amma har yanzu akwai wasu sassan yankin na arewa maso yammaci da ‘yan bindigar kan far ma a kai-a kai.

Ko a makon da ya gabata, wasu matasa sun gudanar da zanga zanga a wasu yankunan Katsina inda suka yi kone-kone don nuna fushinsu kan yadda ‘yan bindigar ke kai masu hari babu kakkautawa lamarin da ke sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi baya ga cin zarafin mata da ake yi.

A can can arewa maso gabashin kasar ta Najeriya kuwa, 'yan Boko Haram da mayakan ISWAP mai alaka da kungiyar IS su ma sun zafafa hare-harensu.

A baya-bayan nan, rahotanni na nuni da cewa hari uku aka kai wa ayarin motocin gwamnan jihar Borno, Prof. Babagana Umara Zulum, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Gabanin harin da aka kai wa gwamnan na baya-bayan nan, mayakan na Boko Haram sun kashe wani babban kwamandan sojin Najeriya a wani harin kwantan bauna.

Sojojin Najeriya sun kai wasu samame da ake ganin tamkar na darken fansa kan kisan Kanar D.C. Bako.

Su dai jami’an Najeriya sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen yunkurin da suke na ganin sun shawo kan wannan matsala ta tsaro.

An tura jirage da dakarun da dama zuwa yammacin arewacin Najeriya inda aka rika kai wa mafakar mayakan hare-hare ta sama.

Amma har wa yau, akwai rahotani da ke nuna cewa da sauran rina a kaba.

Amma yayin da hakan ke faruwa, ‘yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan bukatar a sauya shugabannin hukumomin tsaron kasar ko akasin hakan.

Wata gamayyara kungiyar dattawan arewa maso gabashin Najeriya, ta aikawa da shugaba Buhari wasika inda suka nemi da ya sauya manyan hafsoshin sojin kasar lura da yadda matsalar tsaron ke so ta sake dagulewa.

Amma wasu daga cikin mazauna yankin, irinsu Abdulkarim Abbas na ganin, bai kamata a gudanar da wani sauyi ba.

“Kafin zuwan wannan gwamnatin Buharin, da su Buratai da sauran manyan hafsohin, kowanne mazaunin Maiduguri ya san halin da take ciki,” yana mai cewa al’amuran tsaro sun lalace a lokacin sai bayan da gwamnatin Buhari ta zo.

“Ina ga (a yanzu) zan ce an samu zaman lafiya kashi 70 cikin 100.” In ji Abbas.

Sai dai a irin mahangar mai sharhi kan harkar tsaro Dr. Garus, ya ce akwai bukatar a sallami hafsoshin.

A cewarsa, ba a taba barin manyan hafsoshin su zauna a mukamansu har na tsawon shekara shida ba.

Ya kara da cewa, kamata ya yi su yi shekara biyu saboda su ba da damar da za a nada wasu da ke bayansu domin su ma zo su ba da tase gudunmowar.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina, domin jin cikakkiyar muhawarar da aka yi kan kiran a sauya hafsoshin ko akasin haka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG