Taron Wanda za’a shafe mako guda ana tattaunawa, zai yi nazari akan amfani da ingantattun hanyoyin sadarwa wajen magance tsatsauran ra’ayi dake haddasa tarzoma irin na ta’addanci a kasashen Tafkin Tchadi.
Wannan taron ya tattaro Sojoji da Wakilai daga Majalisar Dinkin Duniya, Majalisar Dinkin Duniya, da Tarayyar Turai, da kuma Shehunan Malamai daga Jami’oin Tafkin Tchadin .
Babban Sakataren Raya Kasashen Tafkin Tchadin, Ambassador Mamman Nuhu, ya bayyana cewa wannan taro zai kuma fito da gaskiyar lamari saboda ‘yan Boko Haram sun dade suna karairayi na cewa sune wannan sune wancan.
Manufa, kada abari sai abu ya rincabe kafin a gane gaskiyan duk da cewa an ci nasarar amfani da karfin soja tun shekaru biyar ko shida da aka fara, wajen dakile ayyukansu.
Ya bayyana cewa, za a ci gaba da amfani da karfin soja kuma an yiwa jama’a bayani yadda matsalar take.Ya kara da cewa idan mutane basu gane ba ai karfin soja ba zai yi nasara ba.
Masu jawabai a taron sun yi ta nanata yadda tarzoman na Boko Haram take rikida ta na daukar wani sabon salo.
Major General Manu Yusuf, Babban Komandan Rundunar Hadin gwiwa na Kasashen Tafkin Tchadi ya bayyana cewa, “Tarzoman da ake fuskanta a Tafkin Tchadi irin na masu tada kayan baya,” Yace wannan ne yasa ake neman sa hannu hukumomin fararen hula domin marawa karfin soji da tuni ake amfani da shi a wannan yanki .
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti:
Facebook Forum