Rashin tsaro a arewacin Najeriya yanzu ya zarce ta’addancin kungiyar Boko Haram da take gudanar da ayyukanta a arewa maso gabashin kasar. Sace mutane da kuma kashe su na kara ta’azzara a cikin wannan lokaci musamman a jihohin arewa maso tsakiya da maso yammacin kasar.
Da alama dai duk matakan da hukumomin tsaron Najeriya ke daukawa a yaki da bata gari basa yin tasiri, ganin yadda su miyagun ke kara samun nasarar kai hare hare a kan talakawa da basu san hawa ba, basu san sauka ba.
A karshen mako ‘yan ta’adda sun kai hare hare a jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna da Naija da kuma Nasarawa. A cewar masu sa ido a kan harkokin arewacin Najeriya an kai wadannan hare haren a cikin sa’o’i 24.
Tsohon shugaban ‘yan jaridar Najeriya, Mallam Nasiru Zaharaddin ya kwatanta hare haren da aka kai cikin sa’o’i 24 da abin ban tsoro. Ya kara da cewa da alamar su ‘yan bindigar da ‘yan ta’adda sun fi karfin hukumomin tsaron Najeriya.
Wani mai bincike kan sha’anin tsaro a Najeriya, Dr. Yahuza Ahmed Getso, da ya ambato danyen aikin da ‘yan ta’addan suka aikata a cikin kwanaki goma, ya ce girman matsalar tsaro a Najeriya ya wuce duk inda ake tunani.
‘Yan ta’addar sun kai hari a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, kana suka yi awon gaba da matar wani farfesa da dansa.
Shi ko Abubakar Ali, masanin tattalin arziki ne wanda ya ce annobar coronavirus ta raunata tattalin arzikin Najeriya, amma matsalar rashin tsaro ka iya ta’azzara lamarin. Ya ce idan rayuwar masu saka jari na cikin fargaba harkar kasuwanci ba zata yiwu ba, kana hakan zai shafi tattalin arzikin kasa.
Sadik Garba Shehu mai ritaya, ya bada shawarar cewa akwai bukatar yin sauye sauye a harkar tsaro, kama daga soja da ’yan sanda da duk hukumomin tsaron kasar.
Ga dai rahoton Hassan Maina Kaina daga birnin Abuja: