Duk da ikirarin da hukumomi ke yi na daukar kwararan matakai kan miyagun da ke kashe jama’a da kuma sace wasu don neman kudin fansa a hanyar Kaduna zuwa Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, har yanzu wannan matsala sai ma abin da ya karu.
Bayan da al’amarin ya dan lafa a baya, yanzu matsalar ta sake tsanani ta yadda mutane ke dada jin tsaron bin wannan hanyar musamman a wasu lokuta da kuma wasu yanayoyi. Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Mataimakin Kwamishina Frank Mba, ya ce lallai su na sane da halin da ake ciki na baya bayan nan kuma duk bai wace irin abubuwan da su ka faru a baya ba. Ya kuma ce, ai su ne su ka fatattaki miyagun a baya, kuma su ne za su sake fatattakarsu.
Mataimakin Kwamishina Frank ya ce da yadda Allah abubuwan da su ka faru kwanan nan a kan wannan hanya sun kusa zama tarihi. Ya ce idan an tuna a baya su ‘yan sandan sun kori miyagun da ke dajin kan hanyar, wadanda su ka hada da ‘yan fashi, da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, da dai sauransu, kuma har yanzu su na da azama da kwarewar yin hakan, kuma za su yi.
To saidai wani dan Majalisar Wakilai daga jahar Naija, Honarabul Muhammed Umar Bago, ya ce gaskiyar magana ita ce: gwamnatinsu ta APC ta gaza. Ya ce au ba a gaya ma Shugaba Muhammadu Buhari gaskiya, au ana gaya masa amma bai daukar abin da muhimmanci. Ya ce an yi mako guda ‘yan ta’adda na tare hanyar Kaduna zuwa Abuja su na kama mutane. Ya ce me zai hana a kai dajin kasa dungurungum? Ya duk wani abu – kama daga gidaje zuwa duk wani abun da ke dajin a kwantar da su da karfin soji. Wannan, inji shi, shi ne maganin wannan matsalar.
Shi kuwa wani masanin tsaro, Guruf Kyaftin Sadik Garba Shehu (murabus), ya ce gaskiyar magana shi ne Najeriya ba ta da isassun sojoji da ‘yan sanda. Kuma wannan magana ce ta samun wadanda za su yi aikin.
Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton: