Kakakin rundunar kanar Timothy Antiga ya shaidawa Muryar Amurka cewa, dakarun MNJTF runduna ta uku sun farma mayakan na yan ta'adda ne daga bangaren Najeriya da manyan bindigogi.
Rahotanni dai sun tabbatar da sojojin rundunonin biyu sun yi wa yan ta'adda barna sosai yayin wannan gumurzu.
Kanar Timothy Antiga yace koda yake kawo yanzu ba a tantance girman barnar da aka yiwa kungiyar ISWAP, to amma bayanan farko da aka tattaro ta hanyar na'urori ya nuna an yi wa masu ikirarin jihadin gagarumar barna.
Wani masanin tsaro a yankin tafkin chadin, Dr. Abubakar mohammed Sani yace muddin dakarun suka ci gaba da kai irin wannan hari na hadin gwiwa ta sama da kasa, to ba shakka za a kawo yan ta'addan.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:
Facebook Forum