Hukumar lafiya matakin farko ta Najeriya wato NPHCDA, ta kawar da fargabar yiyuwar ‘yan kasar ba za su so a yi musu allurar rigakafin cutar Korona birus ba.
Mayakan Boko Haram da ba a tantance adadin su ba sun fice daga garin Dikwa kafin isowar sojoji bayan kwashe tsawon sa’o’i suna rike da iko a garin tare da hana shige da fice.
Babban kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC ya janye batun kara farashi a kan kowacce litar mai da ya shirya yi daga ranar 1 ga watan Maris, bayan zama da masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur din.
Sabuwar babban daraktar hukumar kasuwanci ta duniya wato WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, za ta fara aiki gadan-gadan a hukumar yau litinin 1 ga watan Maris, Shekarar 2021.
‘Yan bindiga sun saki yaran makarantar sakandaren kimiyar gwamnati ta Kagara da ke karamar hukumar mulkin Rafi ta jihar Neja.
‘Yan bindiga a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya sun kai farmaki a wata makarantar sakandaren 'yan mata da ke garin Jangebe a karamar hukumar mulkin Talata Mafara, inda suka yi awon gaba da daliban makarantar.
Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bayyana sace ‘yan matan makarantar sakandaren Jangebe a jihar Zamfara a matsayin take hakki da 'yancin yara.
Hadakar kungiyoyin masu fataucin kayan abinci da dabbobi musamman daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya, ta fara yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar.
‘Yan bidndigar da suka sace yaran kwalejin kimiyar gwamnati ta Kagara 27 da malamai 15 a jihar Neja sun yi barazanar kashe su da yunwa muddin ba a biya su kudin fansa da suke bukata ba a kan lokaci.
Hadakar kungiyoyin arewa ta sake jaddada goyon bayanta ga yunkurin sulhunta rikici tsakanin gwamnati da 'yan bindiga da Sheikh Gumi ke yi.
Masana a faninin sufurin jiragen sama suna ta tofa albarkacin bakin su kan harkokin da suka shafi lafiyar jiragen sama biyo bayan faduwar jirgin rundunar sojin saman Najeriya wanda ya yi sanadiyar mutuwar matukan da sauran mutanen da ke ciki su 7
Bayan rikicin da ya barke tsakanin Hausawa mazaunan jihar Oyo da ‘yan kabilar yarbawa a kasuwar shasha dake birnin badun, masu ruwa da tsaki a Najeriya da suka hada da lauyoyi, iyaye sun bukaci ‘yan kasa su kwantar da hankalinsu tare da gujewa ramuwar gayya.
Kungiyar dattawan arewa ta yi kira ga gwamnonin yankin da su samawa makiyaya matsuguni sakamakon yadda aka bada wa’adin su fice daga wasu sassan Najeriya.
Hukumomin a Najeriya na bayyana damuwa kan karuwa da ake ci gaba da samu a adadin masu kamuwa da cutar korona birus a kasar inda cibiyar kula da cututtuka masu saurin yaduwa ta NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutane dubu 1 da 56 da suka kamu da cutar a ranar talata kadai.
Ministar ayyukan jinkai ta Najeriya ta ce shirin kadamar da horon sa ido na zamantakewa zai taimakawa 'yan Najeriya kusan miliyan 13 a jihohi da dama.
Hukumar hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya NITDA, da hadin gwiwar ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani, ta kaddamar da aikin gina cibiyar kere-keren fasahohin zamani da kasuwanci.
‘Yan kasuwa na kokawa kan rufe kasuwar Wuse, Abuja sakamakon yadda wasu ’yan kasuwa suka ki mutunta ka’idojin kare kai daga Coronavirus.
‘Yan Najeriya na bayyana ra’ayoyin su game da yiyuwar gwamnatin kasar ta dawo da tallafin man fetur sakamakon tashi a farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Majalisar Dokokin Najeriya ta ce dole hafsosin tsaron kasar su sauka, saboda gazawarsu wajen samar da tsaro.
Tun bayan zanga zangar EndSARS batun makomar dunkulewar Najeriya a matsayin kasa daya al'umma daya ya sake zama wani abin takaddama. Yayin da wasu ke ganin kamata ya yi a raba, wasu na ganin rigimar rabawar ta ma fi matsalar zama tare muni.
Domin Kari