Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Arewa Ku Shirya Karbar Makiyaya - Kungiyar Dattawa Arewa Ta NEF


Nastura Ashir Sharif
Nastura Ashir Sharif

Kungiyar dattawan arewa ta yi kira ga gwamnonin yankin da su samawa makiyaya matsuguni sakamakon yadda aka bada wa’adin su fice daga wasu sassan Najeriya.

Tun ba yau ba al’umman arewa ke ta yin kira da shugabannin su kan samawa fulani makiyaya matsuguni da zasu rinka kiwo cikin walwala don kawo karshen rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, a wannan karo bayan rashin jituwa da ya kai ga rasa rayuka da dukiyoyi daga bangarorin biyu musamman a kudancin Najeriya.

Kungiyar dattawan arewa ta yi kira ga gwamnonin yankin da su samawa makiyaya matsuguni sakamakon yadda aka bada wa’adin su fice daga wasu sassan Najeriya, ta bakin kakakin ta Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ta na mai zargin cewa, wasu kungiyoyi marasa kishin kasa ke ruruta wutan rikici domin cimma mumunan manufar su.

Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin Arewa, Nastura Ashir Shariff, ya ce kusan kullum sai ya samu kiran waya daga mutane a dazuzzuka suna gaya musu yadda ake kashe musu mutane da dabbobinsu daga wadanann yankuna, kana wasu sun fara baro yankunan amma ana kama su ana kashe su.

Babu yadda za’a yi ace kundin tsarin mulkin kasa ya na bawa wasu mutane kariya ba zai bawa wasu mutane kariya ba, to mafi alheri su tattara su dawo, su gwamnonin arewacin Najeriya tun da a cikin su kamar gwamanonin jihar Kogi, Neja Zamfara da kuma Kano, sun ce suna da wurare da za su iya tanada inda za su yiwa makiyayan nan wurin da za su zauna, duk mutumin da ya ce za’a yi rashin adalci a zauna lafiya karya yake yi,” a cewar Nastura Ashir.

A wani bangare kuma, gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi, ya ce ba wa makiyaya wa’adin su fice daga wasu sassan Najeriya bai dace ba.

Dan majalisar wakilai, mai wakiltar mazabar Yamatu Deba na jihar Gombe, Alhaji Yunusa Ahmad Abubakar, ya ce wannan lamari da aka shiga ciki wato yana daya daga cikin hanyoyin da ya ke juya bayinsa kuma ya nuna musu irin kura-kuran da suke yi.

Alhaji Yunusa ya kara da cewa arewa yadda muke a da ana zaune da makiyayan nan, amma gwamnatoci da suka shude muna da abin da ake kiransu "grazin reserve," to nan za’a shiga ayi kiwo akwai wadansu wurare da ake burtali to duk wadanan abubuwa sai kawai aka wayi gari duk sun shude. ba’a lura da hakkoki na dan adam ba.

Tun bayan dawowa tsarin mulkin dimokradiyya a shekarar 1999 ne aka fara samun rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya, lamarin da baya rasa nasaba da shigan gonaki da shanu abun da ake ganin ya na neman ya gagari gwamanti ta hanyar tsananta matsalolin tsaro.

Sai dai duk kokarin ji ta bakin gwamnati a kan matakin kare rayukan makiyaya da ke ficewa daga sassan da aka basu wa’adin su fice din ya ci tura.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG