Alkaluma daga cibiyar NCDC dai sun yi nuni da cewa adadin wadanda suka kamu da cutar korona birus a Najeriya tun bayan bullar ta ya kai dubu 141 da 447, kuma wadanda ke fama da cutar a cibiyoyin kula da masu dauke da cutar a yanzu sun kai dubu 23 da 998.
Babban manajan kula da lamurran yaki da cututtuka na cibiyar NCDC, Dakta Mukhtar Muhammad, ya yi karin bayani a kan karuwa da ake samu, ya ce suna da masaniya kan gudunmuwa da kamfanin BUA ya bayar na sayo rigakafi milyan 1 kyauta ga yan Najeriya.
Jimilar wadanda suka rasa ransu sakamakon cutar corona a yanzu dai ya kai dubu 1 da 694 kuma alkaluman jiya talata sun yi nuni da cewa jihar Legas ke kan gaba da wadanda suka kamu da cutar 214, sai jihar Osun mai 120, birnin tarayya Abuja mai adadi 116 da dai sauransu.
Tun bayan bullar cutar a Najeriya dai, cibiyar NCDC ta gudanar da gwaji kan samfurin mutane milyan 1 da dubu 398 da 630.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra'uf cikin sauti: