Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sace Daruruwan Dalibai Mata a Makarantar Sakandaren Jihar Zamfara


Was makamai da aka Kama a hannun 'yan bindga.
Was makamai da aka Kama a hannun 'yan bindga.

‘Yan bindiga a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya sun kai farmaki a wata makarantar sakandaren 'yan mata da ke garin Jangebe a karamar hukumar mulkin Talata Mafara, inda suka yi awon gaba da daliban makarantar.

Kwamishinan yada labarai na jihar ta Zamfara, Suleiman Tunau Anka, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce ‘yan bindigar sun afkawa makarantar da misalin karfe 2 na dare a yau Juma’a tare da yin awon gaba da yaran makarantar.

Sai dai Suleiman Anka bai tabbatar da adadin 'yan matan da ‘yan bindigar suka sace ba.

Amma wani malamin makarantar, Sadi Kawaye, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, dalibai sama da 300 ne ba'a gani ba a yayin da aka kidaya saura dalibai bayan wucewar 'yan bindigar.

Wasu shaidun gani sun ce 'yan bindigar sun soma da harbi a iska ne inda suka tsorata jama'ar garin, kafin kutsawa cikin makarantar.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan banga sun gwada tunkarar 'yan bindigar, amma kuma sun kasa saboda yawan 'yan bindigar da aka ce sun fi 100.

Duk kokarin jin ta bakin hukumomin tsaro a jihar ta Zamfara a yayin hada wannan rahoton ya ci tura.

Wannan kuma na zuwa ne kwanaki 9, bayan da wasu 'yan bindigar suka yi awon gaba da dalibai da malamai a makarantar sakandare ta Kagara a jihar Neja, wadanda har yanzu ba sako su ba.

Zamfara na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fuskantar ukubar 'yan bindiga.

Karin bayani akan: AFP, jihar Zamfara​, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG