Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNICEF Ta Yi Allah Wadai Da Sace ‘Yan Mata A Zamfara


Shelkwatar UNICEF.
Shelkwatar UNICEF.

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bayyana sace ‘yan matan makarantar sakandaren Jangebe a jihar Zamfara a matsayin take hakki da 'yancin yara.

A sanarwa da ya fitar, wakilin asusun na UNICEF a Najeriya Peter Hawkins, ya yi Allah wadai da harin da ya auku a yammacin Najeriya, wanda shi ne irin sa na biyu a cikin kasa da makwanni biyu.

Wasu 'yan bindiga sun kai irin wannan hari a jihar Neja, inda suka yi makaranta na yara maza.

Peter Hawkins ya kara da cewa asusun UNICEF na kan aikin tantance adadin yaran da ‘yan bindiga suka sace wanda a halin yanzu ake cewa sun kai sama da 300.

Hawkins ya bayyana bakin ciki da wannan mumunan hari da aka kaiwa yaran makarantar mata a Najeriya ya na mai kwatanta sabawa tunani wanda ka iya yin tasiri sossai a kan lafiyar kwakwalwar yaran.

"Kamata a ce yara sun samu kwanciyar hankali a gida ko a makaranta kuma bai kamata iyaye su kasance cikin fargaba a duk lokacin da suka tura yaran su makaranta ba da safe", in ji Peter Hawkins.

Asusun UNICEF ya yaba da kokarin gwamnatin Najeriya na tabbatar da kubuto yaran makaranta tare da yin kira da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su ninka kokarinsu don tabbatar da cewa, an kubutar da yaran cikin koshin lafiya.

Karin bayani akan: Peter Hawkins, UNICEF, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG