Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Boko Haram Sun Fice Daga Garin Dikwa Na Jihar Borno


Wani Hoton Mayakan Boko Haram
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:12 0:00

Wani hoton mayakan Boko Haram (AFP).

Mayakan Boko Haram da ba a tantance adadin su ba sun fice daga garin Dikwa kafin isowar sojoji bayan kwashe tsawon sa’o’i suna rike da iko a garin tare da hana shige da fice.

Wata Majiya daga garin na Dikwa ta bayyana cewa, mayakan na Boko Haram sun shiga garin da motocin yaki sama da 20 makare da bindigogin kakkabo jiragen sama da yammacin ranar Litinin, domin shawo kan dakarun soji.

Haka kuma sun lalata wasu gine-ginen gwamnati da suka hada da cibiyar kiwon lafiya matakin farko, sakatariyar karamar hukuma, wani bangare na fadar masarautar Dikwa da kuma cibiyar majalisar dinkin duniya.

Gwamnan Jihar Borno, Prof. Babagana Umaru Zulum
Gwamnan Jihar Borno, Prof. Babagana Umaru Zulum

Mayakan dai sun fice daga garin ne da misalin karfe 11:15.

Mazaunan yankin sun bayyana cewa sun dan samu kwanciyar hankali a halin yanzu bayan ficewar mayakan da aka ga sun nufi hanyar garin Marte, suna cewa, dakarun rundunar sojin saman Najeriya za ta iya bin sawu domin fatattakar su.

A halin yanzu dai, ba a tantance adadin mutanen da mayakan suka yi awon gaba da su ba.

Dubban fararren hula ne suka tsinci kan su cikin wannan mumunan yanayi na zama ba fita ba shiga a hannun mayakan na Boko Haram tun da suka kwace iko da garin da maraicen jiya Litinin.

Haka kuma, majiyar ta bayyana cewa, da maraicen jiya sojoji sun dakile harin da mayakan suka kai garin kafin daga bisani bayan wasu sa’o’i mayakan suka dawo kuma suka shawo karfin dakarun dake tsare da garin.

Jaridar Daily Trust ya ruwaito, mazaunan garin suna cewa sun ga mayakan na sintiri a unguwanni garin tare da yiwa yan garin nasiha kan kada su firgita su kuma fice daga garin, inda suke cewa, sojoji su ka kawo wa farmaki ba ‘yan garin ba kuma suna tare da su.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun rundunar soji suka sake daura damarar kwace ikon garin daga hannun mayakan Boko Haram.

Garin Dikwa wanda ke kusan nisan kilomita 90 daga birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar dai ya fuskanci hare-haren mayakan Boko Haram da dama tun bayan kwace ikon garin daga hannun su tun shekarar 2016.

Kazalika, garin na Dikwa ne mazaunin sansanin dakarun rundunar soji na musamman na 9, inda babban hafsan sojin Najeriya ya kai ziyara a makon jiya, ya kuma ba da umarnin dakarunsa su kwace ikon garin Marte dake da nisan kilomita 20 daga sansaninsu daga hannun mayakan Boko Haram.

Karin bayani akan: jihar Borno, Boko Haram, Dikwa, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG