Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da 'Yan Najeriya Ke Cewa Kan Yiwuwar Maido Da Tallafin Man Fetur


‘Yan Najeriya na bayyana ra’ayoyin su game da yiyuwar gwamnatin kasar ta dawo da tallafin man fetur sakamakon tashi a farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Tun bayan kara kudi kan farashin litar man fetur a watan Nuwamban shekarar 2020 a Najeriya ne farashin gangar mai a kasuwannin duniya ke ta karuwa daga dala 41 da digo 51 zuwa dala 51 da digo 22 a watan disamba.

Hakan ya sa dilallan man fetur a kasar suke duba yiyuwar kara kudi a kan farashin kowacce lita, sai dai gwamnatin tarayya ta sanar da rage naira biyar kan kowacce lita abin da bai ma dilalan man dadi ba saboda gwamnati ta ce ta bar mu su ragamar kayyade farashin mai a baya.

Da muka tuntubi tsohon shugaban kungiyar dilalan man fetur na Najeriya, Musa Felande, ya ce batun dawo da tallafin man fetur bai taso ba.

Wakiliyar Muryar Amurka Halima Abdul’Rauf ta tuntubi wasu ‘yan kasa abinda suke gani da batun yiyuwar dawo da tallafin man fetur sakamakon tashin farashin danyen mai a Najeriya.

Idan ba a manta ba, ‘yan Najeriya sun fuskanci kari a farashin kowacce litar man fetur a cikkin watanni kudu daga naira 121 da digo 50 zuna Naira 123.50 a watan Yuni, daga N140.80-N143.80 a watan Yuli, Naira 148-N150 a watan Agusta, N158-N162 a watan Satumba da kuma Naira 163-N170 a watan Nuwamba.

Kazalika, a watan Satumban shekarar 2020 ne karamin ministan albarkantun man fetur, Timipre Silver, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta cire hannun ta kan batun kayyade farashin man fetur yana mai cewa, nauyin kayyade farashin man fetur ya koma kan dilallan man fetur da yanayin farashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya.

Duk kokarin ji ta bakin gwamnatin Najeriya da kamfanin man fetur ya cutura.

Saurari cikakken rahoton da ra’ayoyin wasu ‘yan kasar da Halima Abdul’Rauf ta aiko mana:

‘Yan Najeriya Sun Bayyana Ra’ayoyi Su Game Da Yiyuwar Tallafin Man Fetur Daga Gwamnati
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


XS
SM
MD
LG