Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce kamfanin Twitter ya amince da dukkan sharuddan da ta gindaya na gudanar da ayyukansa a kasar.
A yayin da ake dakon farar takardar rahoton kwamitin duba zargin kashe masu zanga-zangar ENDSARS a Lekki, karamin ministan kwadago, Festus Keyamo, ya caccaki kwamitin da aka kafa domin binciken laifukan cin zarafi da kisan gilla da ake yiwa 'yan sanda a zanga-zangar ENDSARS.
Hukumar kula da cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta ce tana sa ido kan bayanan da ke fitowa kan sabon nau'in cutar COVID-19 na Omicron, wanda aka fara ganowa kwanan nan a kasar Afirka ta kudu.
Jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa a watan Fabrairun 2022 za a yi babban taronta na kasa.
Kungiyar matan shuwagabannin kasashen nahiyar Afrika kan zaman lafiya ta gudanar da taron yini guda karo na 9 wanda uwargidan shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari ta karbi bakuncinsa a wannan karon a birnin tarayyar kasar Abuja.
Jihar Kano ta tara makudan kudaden shiga a matsayin haraji wato VAT fiye da daukacin shiyyar Kudu maso Gabas a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2021 kamar yadda wata takarda ta hukumar FIRS ta tabbatar.
Wani Dillalin Miyagun Kwayoyi Da Ya Boye Hodar Ibilis A Ban Dakin Filin Tashi Da Saukan Jiragen Saman Legas Ya Shiga Hannu
‘Yan bindiga da ba a iya tantance iya adadinsu ba sun koma tare hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka afka wa matafiya tare da harbe wani tsohon dan takarar gwamna a jihar Zamfara, Alhaji Sagiru Hamidu, tare da sace wasu da dama.
Har yanzu tsuguni ba ta kare ba a game da batun neman mafita kan halin tsaro da yanayin da makarantun yankin arewacin Najeriya ke ciki.
Fitaccen marubuci kuma mai karantarwa a Najeriya, Mal. Khalid Abdullahi Zaria ya ce kusan kullum ana yin musu a kan abubuwan da suka shafi tarihi a kasar, kama daga kaka da kakanni, addini, zuwan bayajidda da dai sauransu.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karbi takardar neman shiga tsarin samun gida guda dubu 7 da 315 na tsarin gidajenta guda dubu 5 da aka gina a karkashin shirin gidaje na kasa mako daya da kaddamar da aikin.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya za ta jiran gwamnatocin jihohi su aiwatar da tsarinsu a game da rahoton ENDSARS, don haka za ta jira sanarwa daga gwamnatocin jihohin kasar da suka kafa kwamitin bincike kan ayyukan cin zarrafin ‘yan sanda a kasar.
Yajin aikin gargadi na kwanaki uku da ma'aikatan hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya wato NRC suka yi ya hana zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasar.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da akalla mutane biyar a wani kamfanin ruwan leda a garin Tegina da ke karamar hukumar Rafi na jihar Naija.
Akalla ma’aikatan hukumar ICPC 50 ne suka bayyana a gaban wani kwamitin hukumar kan tantance takardun shaidar karatu da bayanan hidima inda aka gano wasu kura-kurai a shekarun su da kuma takardun shaidarsu na kammala karatu.
Ministan shari’a kuma antoni janar na tarayyar Najeriya, Abubakar Malami, ya sake nesanta kansa da ofishin antoni janar daga madugun wadanda ake zargi da hannu a kutsen da aka kai gidan alkaliyar kotun koli mai shari’a Mary Odili.
Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa fasakwauri ne ke haddasa tashin farashin shinkafa a Najeriya.
Rahotanni daga jihar Borno sun yi nuni da cewa akasarin ‘yan gudun hijirar da ke zama a sansanin Bakassi sun bayyana aniyarsu ta komawa gida da kuma komawa gudanar da ayyukan noma domin samun abin dogaro da kai maimakon dogaro da dan kankanin kayan agaji da ake ba su.
Rundunar yan sandan Najeriya ta sami nasarar kama mutane 14 da ake zargin suna da hannu a kutsen da aka kai gidan babbar jojin kotun koli, mai shari’a Mary Odili, da ke birnin Abuja a ranar Alhamis.
Domin Kari