Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya 7,315 Sun Cika Takardar Neman Gida A Shirin Rukunin Gidaje Na Gwamnatin Tarayya


Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karbi takardar neman shiga tsarin samun gida guda dubu 7 da 315 na tsarin gidajenta guda dubu 5 da aka gina a karkashin shirin gidaje na kasa mako daya da kaddamar da aikin.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake yiwa mambobin kwamitin majalisar dattijai mai kula da gidaje bayani kan shirin samarwa yan kasa gidaje.

A karshen makon jiya ne gwamnati ta kaddamar da shafin yanar gizo na shirin samar da gidaje ga yan Najeriya mai dauke da tsarin daki daya, dakuna biyu da ma uku a birnin tarayyar kasar, Abuja in ji Fashola.

Minista Fashola ya ce daga cikin sama da mutane dubu 7 da 315 na ‘yan Najeriya da suka karba a ranar Alhamis, akwai dubu 7 da 216 basu kamalla cika takardar zuwa karshe ba, yayin da mutane 99 suka cika 100 bisa 100.

Haka kuma, Fashola ya bayyana cewa a cikin wadanda suka cika takardar neman gidajen mutane 24 suka gabatar da bukatunsu daga babban birnin tarayya Abuja, kuma babu ko mutum guda daya da ya shiga shirin daga jihohi 20 na kasar.

Ministan dai ya kara da cewa shirin samar da gidajen na kasa na yanzu wani shiri ne na gwaji da aka bullo da shi da nufin shigar da masu zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu dama ciki don samawa yan Najeriya sauki a fannin samin gidaje a sauwake a kasar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A game da gibin da ake samu a fannin samar da gidajen ga yan kasa, ministan ya shaidawa kwamitin majalisar dattawa mai kula da gidaje da sanata Sam Egwu ke jagoranta cewa mafita ba wai kawai a gina gidaje ba ne har da tallata wadanda babu kowa a ciki da aka gina a baya.

Fashola ya kara da cewa a baya shirin samar da gidaje na kasa bai yi nasara ba kuma wasu gidajen da aka gina a baya din har yanzu babu kowa a cikinsu lamarin da baya rasa nasaba da yanayin al’adu ko rashin kudin biya a tsarin da aka fitar.

Gwamnatin Najeriya dai na da shirin samar da gidaje na kasa da ma’akatan gwamnati za su iya shiga don samun mahalli da zasu rika cirewa daga cikin albashinsu na wata-wata har su gama biya su mallaki gidajen.

Sai dai ba kowanne ma’aikaci zai iya shiga tsarin ba sai sun kai matakin da gwamnatin kasar ta tsara wanda zai yi daidai da albashin da su ke samu.

XS
SM
MD
LG