Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Kano Ta Sha Gaban Kudu Maso Gabas A Tara Kudaden Shiga


Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)

Jihar Kano ta tara makudan kudaden shiga a matsayin haraji wato VAT fiye da daukacin shiyyar Kudu maso Gabas a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2021 kamar yadda wata takarda ta hukumar FIRS ta tabbatar.

Bayanai na karbar harajin kayayyaki wato VAT daga hukumar tara harajin cikin gida ta Najeriya wato FIRS, sun yi nuni da cewa jihar Kano ta tara naira biliyan 24 da miliyan 400, inda ta sha gaban jihohin Kudu maso gabas biyar da suka tara naira biliyan 20 a jimlance kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Bayanan sun nuna cewa jihar Kaduna da ta samu tattara harajin VAT na naira biliyan 19, ita ma ta sha gaban jihohin Akwa Ibom da ta tara naira biliyan 9.3, Bayelsa mai harajin naira biliyan 13, Delta ma naira biliyan 13, sai jihar Edo mai naira biliyan 9, da kuma Ogun mai naira biliyan 11.

Haka kuma, harajin Naira biliyan 19.8 na jihar Kaduna ya zarce na jihohin Abia, Cross Ribas, Osun, Ekiti, Ondo da kuma Imo.

A bisa ga alkaluman kididdiga jihar Abia ta tara naira biliyan 2 da miliyan 2 wanda ke kwatankwacin kaso 0.22, Kuros Riba ta tara naira biliyan 1 da miliyan 9 kwatankwacin kaso 0.19%, Osun ta tara naira biliyan 2.07 ko kuma kwatankwacin kaso 0.20, sai Ekiti ta sami naira biliyan 6 da dubu 200 kwatankwacin kaso 0.62, Ondo ta samu naira biliyan 4 da miliyan 800 kwatankwacin kaso 0.48, yayin da jihar Imo ta tara naira biliyan 1 da digo 01 kwatankwacin kaso 0.10 %.

Jihar Yobe dake arewa maso gabas ta tara naira biliyan 9 da miliyan 300 inda ta ke gogayya da jihar Akwa Ibom mai naira biliyan 9 da miliyan 300, sai Edo mai naira biliyan N9, Ebonyi naira biliyan 7 da miliyan 200 sai jihar Ekiti mai harajin naira biliyan 6 da miliyan 200.

Jihar Legas da babban birnin tarayya, sun ba da kashi 65. 22 na jimillar harajin, yayin da sauran jihohi 35 suka ba da kashi 34.78 a jumlance.

Wannan bayanin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-ku-ce tsakanin gwamnatin tarayya da wasu jihohi, da kuma zargin cewa wasu jihohin, musamman a Arewa, sun fi cin moriya daga lalitar tarayya abun da ya zarce gudummawar da su ke bayarwa.

Alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa Legas ce ke kan gaba da kaso 41 da digo 5 na adadin harajin VAT wanda ya kai naira biliyan 421 da miliyan 200 yayin da Zamfara ta tara mafi karancin haraji na Naira miliyan 762 da digo 5 kwatankwacin digo 0.08 na jimillar kudaden.

Babban birnin tarayya Abuja ne ke biye da Lagos wanda ya tara naira biliyan 24.ko kwatankwacin kaso 23 da digo 74, Ribas ta karbi Naira biliyan 92.3bn kwatankwacin kaso 9.09 yayin da Oyo ta biye da biliyan 61bn wanda ke kwatankwacin kaso 6 da digo 01.

Sauran wadanda ke kan gaba a jadawalin sun hada da jihar Kano dame harajin nairan biliyan 24 da miliyan 400 ko kwatankwacin kasi 2.40, sai Kaduna da nairan biliyan 19.8bn ko kuma kwatankwaci kaso 1.95.

Sai dai duk da cewa jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma ba ta tara wani harajin a zo a gani ba, wasu jihohin arewa sun fi jihohin Kudu samar da harajin kamar yadda alkaluman kididdigar suka nuna.

Duk da rikicin da ake fama da shi a wasu jihohin Arewa maso Gabas, yankin ya tara jimillar naira biliyan 27 da miliyan 700 idan aka kwatanta da naira biliyan 21 da yankin kudu maso gabashin kasar ya tara.

Baya ga jihar Legas, sauran jihohin Kudu maso Yamma sun tara jimillar naira biliyan 85 da miliyan 800 kawai yayin da Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da ke fama da tashe-tashen hankula da sauran kalubalen tsaro sun tara naira biliyan 86 da miliyan 5bn a cikin lokaci guda.

Jihar Legas dai na da naira biliyan 421 da miliyan 200, Ribas naira biliyan 92 miliyan 3bn, Sai Oyo naira biliyan 61, Kano da naira biliyon N24 da Kaduna na da nara biliyan 19, inda alkaluman saka yi suni da cewa mafi yawan jihohin sun nuna matsakaicin tara harajin na kasa da naira biliyan 10.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG