Karamin ministan kwadago da ayyuka, Festus Keyamo, wanda mamba ne a kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin tattaunawa da kafar sada zumuntar yanar gizo, wand ya bayyana hakan a lokacin da ya bayyana a cikin wani shirin gidan talabijin na Channels.
Keyamo ya ce kwamitin ya samu gaggarumin ci gaba sosai a tattaunawa da ya ke yi da kamfanin Yuwita kan lamarin.
Haka kuma, Keyamo ya ce shugaban Najeriya ya dauki mataki kan kamfanin Tuwitan ne don sake daidaita dangantakar kasar da Tuwita ba wai don kore su daga kasar ba ne, kuma an sake fasalin kwamitin ne da sanya Keyamo a ciki ne don cimma manufar kafa shi.
A cewar Keyamo, an kuma kafa wani karamin kwamitin mambobi masu ilimin fasahar zamani da zai yi mu’amala da kamfanin Tuwita tare da samar da wasu sharudda da dama domin su cika su saboda a dage dakatarwar da aka yiwa kafar a Najeriya.
"Kamfanin Tuwita ne ya tuntubi gwamnatin tarayya inda suka ce suna son sanin mai zasu iya yi don daidaita dangantakar da ke tsakanin kafar da gwamnatin Najeriya don haka kamfanin ya cika sharudda da aka gindaya masa kuma ya amince da dukkansu" in ji Keyamo.
Idan ana iya tunawa, a yayin gabatar da jawabi a zagayowar ranar samun ‘yancin kan Najeriya, shugaban Muhammadu Buhari ya ce dole ne kamfanin Tuwita ya cika sharudda biyar kafin a dage dakatarwar da aka yi masa a kasar.
Sharuddan dai sun hada da kafar Tuwita ta mai da hankali kan tsaro da hadin kai na kasa, yin rijistar kasancewarsa da wakilcinsa a Nijeriya, biyan haraji, tabbatar da hanyar warware rikici ta yadda ya dace da gudanar da ayyukanta daidai da tsarin cikin kasar.
A ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2021 ne gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta haramta yin amfani da shafin Tuwita a kasar sakamakon goge sakon da shugaban ya wallafa a shafinsa na Tuwita game da masu tada kayar baya saboda yadda wasu ‘yan Najeriya suka bayyana sakon na sa a matsayin mai tunzura jama’a.