Yan sanda a Bangladesh sun ce sun kama Shahidul Alam, wani sanannen mai daukar hoto, akan irin sakonnin da yake sanyawa a shafin Facebook da wasu shafukan sada zumuncin gameda zanga-zangar da dalibai suka yi a Dhaka, babban birnin kasar, inda suke yin kira akan a aiwatarda dokokin hanya, a kuma kara kiyaye masu tafiya a kasa a kusa da makarantu.