Gamsuwa da irin abubuwan da suka gani a yayin ziyarar da suka gudanar ranar Alhamis, a wasu kauyukan Maradi inda jama’a suka bada kai akan maganar yaki da talauci da yaki da karancin abinci da kuma yadda a fili ake gane kyakkyawar aniyar mahukuntan Nijar akan maganar inganta rayuwar mazaunan karkara, ya sa shuwagabanin FAO da IFAD wato FIDA da PAM ko WFP yin na’am da bukatar gwamnatin Nijar domin daukar dawainiyar ayyukan dake kunshe a wani tsarin ci gaba mai dorewa inji shugaban asusun IFAD Gilbert F. Houngbo a taron manema labaran da suka kira.
Jami’an hukumomin MDD dake kula da sha’anin abinci a yayin wannan ziyara ta karkarar Nijar sun bayyana cewa sun ga abubuwa da dama da ke kara tabbatar masu da cewa mata na da rawar takawa wajen ciyar da wannan kasa gaba, bisa la’akari da yadda mata a karkara ke aikin farfado da kasar noma domin samarwa kansu dogaro da kai. a cewar MME Kane Aishatu Bula, ministar fasalin kasa.
Rashin ruwa kusa da jama’a na daga cikin matsalolin dake haddasa damuwa a rayuwar mutane a karkara, lamarin dake haifar da cikas ga karatun ‘yan mata, wanda a karshe ke zama dalilin aurar da su suna karancin shekaru, hakan Kuma na tsundumasu cikin matsalolin haifuwa,wannan dalilin ne yasa hukumomin MDD suka kaddamar da wani shirin tanadin tankin ruwa, domin bukatar jama’a a wani kauye dake Maradi, a matsayin gwajin babban tsarin da aka yiwa suna tankunan ruwa miliyan daya domin jama’a a yankin sahel.
Bada fifiko ga ayyukan noma da kiwo domin magance matsalar zaman kashe wando na daga cikin hanyoyin da ake ganin zasu taimaka a cirewa matasa tunanin zuwa cirani wasu kasashen. Haka yasa hukumomin Nijar suka bukaci hadin kan MDD a yayin da MDD ta kawo ziyarar.
Facebook Forum