Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Hada Kai da Wasu Kasashe Don Cimma Yarjejeniyar Nukiliya Da Iran


Mai ba Shugaban Amurka Donald Trump shawarwari kan harkokin tsaron kasa, yau litinin ya bayyana yarjejeniyar nukiliyar kasa da kasa da aka cimma da Iran a matsayin, gurguwar yarjejeniya, ya kuma ce Amurka tana aiki da abokan kawancenta na kasashen Turai da nufin kara matsawa Iran lamba.

John Bolton ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya gabatar a birnin Kudus inda ya gana rana ta biyu jere da Pirai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Bolton yace, hana Iran mallakar makaman nukiliya batu ne da yake da muhimmancen gaske, kuma dalili ke nan da ya sa shugaba Trump ya janye daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, ya kuma sake maida takunkumin tattalin arzikin da aka sawa kasar.

Amurka ta hada kai da Birtaniya da China da Faransa da Rasha da kuma Jamus wajen cimma yarjejeniyar da Iran, da tayi alkawarin rage ayyukanta na nukiliya, ita kuma a saka mata da sassauta takunkuman da aka kakaba mata.

Kamar Trump, Netanyahu shima yana kushewa yarjejeniyar da yace ta ba Iran sausauci mai yawa ba tare da samun wani abin kirki daga Iran ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG