Moshiur Rahman, wani dan siyasa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa an kai Alam ofishin ‘yan sanda da safiyar yau litinin kuma an yi mashi tambayoyi akan ba kafafen yada labarai dabam dabam bayanan karya, da kuma yin kamalan tada husuma. Rahaman ya ce za a dauki matakin doka akan mai daukar hoton.
A kalla ‘yan sandan farin kaya 30 ne suka kama Alam a gidansa da yammacin jiya Lahadi.Masu zanga-zangar sun cigaba da yin arangama da ‘yan sanda jiya, rana ta takwas da fara zanga-zangar, a kokarin da suke yi na neman a gyara dokokin hanya da kare rayukan masu tafiya a kasa.
Haka kuma wasu ‘yan bindiga sun kaiwa wata mota dake dauke da jakadan Amurka a Bangladesh, Marcia Bernicat hari da yammacin ranar Asabar, amma babu wanda ya jikkata a harin.
Facebook Forum