Tsohon shugaban kasar Ghana Jerry John Rowlings ya rasu bayan ya yi fama da jinya a wani asibiti da ke kasar.
Yayin da ake ci gaba da kidayar kuri'u a zaben shugaban kasa a Amurka, kafafen yada labarai sun yi hasashen wanda ya lashe zaben.
A Jamhuriyar Nijar wata sabuwar mahawara ta barke a game da makomar takarar jagoran ‘yan adawar kasar Hama Amadou.
Masu zanga zanga sun fito a garuruwa da dama jiya Laraba don kiran da a kammala kirga kuri’un zaben shugaban Amurka.
An zaku a samu sakamakon zaben Shugaban kasar Amurka, amma ganin yadda aka kada kuri'u da dama ta hanyar aikewa da wasiku, an samu jinkiri wajen kammala kidayar wasu muhimman jahohi, wadanda sakamakonsu ne zai nuna alkibar zaben.
Wata kotu a Mali ta yanke hukuncin kisa ma wani mai ikirarin jihadi da ake zargi, da kuma wani da ake tuhumarsu tare da kashe mutane fiye da dozin biyu a hare hare kan ‘yan kasashen waje a 2015.
A jamhuriyar Nijar, hukumar kula da shige da ficin kaya ta kafa wasu sabbin dokokin aikin fiton kaya da nufin magance matsalolin da ake fuskanta a tsakanin jami’an kwastam da ‘yan kasuwa da kuma masu aikin sufuri.
Hukumar kula da kafofin yada labarai ta Najeriya wato NBC, ta ce tana tuhumar tashoshin talebijin uku masu zaman kansu da zargin taka rawa wajen fadada tashe tashen hankula a kasar biyo bayan zanga zangar EndSARS.
Shugabannin al'umma da addinai da kabilu a jihar Sokoto sun yi kira ga mabiyansu da su zauna lafiya tare da juna domin samar da zaman lafiya a jihar don kauce wa tashin hankalin da ke faruwa a wasu sassan Najeriya.
Wata hatsaniya da ta tashi a titin Ahmadu Bello Way daura da Kasuwar Terminus a tsakiyar birnin Jos hedikwatar jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya tayi sanadin rasa dukiyoyi.
Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masu zanga zangar lumana kusan 12 da jami’an tsaron Najeriya suka harbe har lahira a dandalin mashigar Lekki ya kuma yi alkawarin za a bi musu hakkinsu.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga zanga #EndSARS a wasu sassan manyan birane a Najeriya, gwamnatin jihar Legas ta kakaba dokar hana fita ta tsawon sa’a 24 a duk fadin jihar.
Ma'aikatar Shari'ar Najeriya ta karbi rahoton hukumar kare hakkin bil’adama ta NHRC, mai kunshe da bukatar ayi kora tare da hukunta wasu tsoffin jami’an 'yan sandan SARS.
Ganin yadda zanga zanga da tashe tashen hankula ke neman hana shi yin sakat a kasar, Shugaba Sooranbi Jeenbekov ya yar da kwallon mangoron. To sai dai ba a san ko shin ya rabu da kudar ba.
Ma’aikatan kashe goba sun shiga rana ta biyar yau Alhamis a kokarinsu na kashe gobarar daji a wani gandu a tsaunin Kilimanjaro, wanda shine mafi tsayi a Afirka.
Domin Kari