Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abun Da Ake Nufi Da “Zababben Shugaban Kasa” A Amurka


'Yan takarar zaben a Amurka
'Yan takarar zaben a Amurka

Yayin da ake ci gaba da kidayar kuri'u a zaben shugaban kasa a Amurka, kafafen yada labarai sun yi hasashen wanda ya lashe zaben.

A Amurka, ana kiran Joe Biden na Democrat zababben shugaban kasa.

Zababben shugaban kasa, kalma ce ta kwatance ba ofishi ba ne mai zamansa a hukumance ba. Hakan na nufin Biden, ba shi da karfin iko na gwamnati, har sai an rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairun 2021.

A ranar 7 ga watan Nuwamba, kafafen yada labaran Amurka, wadanda suke bin diddigin kuri’un da ake kidayawa, sun dauki mataimaki Biden, cewa ya ba da tazarar da ba za a iya kamo shi a jihar Pennsylvania ba, abin da ya ba shi damar samun kuri’un kwalejin zabe sama da 270 da ake bukata kafin zama shugaban kasa.

‘Yan mintina bayan tabbatar da hakan, suka yi hangen cewa shi ne wanda ya lashe zaben.

Dalilin kenan da ya sa kafafen yada labarai, ciki har da VOA, suka fara kiran Biden a matsayin “wanda aka yi hangen shi ne ya yi nasara”.

A wasu lokuta, a irin wannan zaben da ake kusan kunnen doki, a kuma lokacin da kafafen yada labarai suka yi irin wannan kira, daya dan takarar ba ya amincewa ya sha kaye. Shugaba Donald Trump shi ma bai yi haka ba, domin yana zargin an tafka magudi ba tare da ya ba da kwararan hujjoji ba kuma ya sha alwashin ci gaba da bin kadinsa.

Matakin shugaban kasar ya raba kan ‘yan majalisa a Washington, abin da ya sa ‘yan Republican ke goyon bayan matakin zuwa kotu don duba zargin an tafka magudi duk da cewa, suna kuma murnar lashe zaben da wasu ‘yan majalisar suka yi a takararsu.

Yaushe Za’a Warware Wannan Takaddama?

Ba za a bayyana sakamakon zaben ba sai nan da makonni. Amma a halin da ake ciki, akwai yiwuwar a kalubalanci sakamakon zaben a kotuna a kuma ba da umurnin sake kirga kuri’un.

Ya zuwa yanzu, gwamnatin Trump ba ta gabatar da wata hujja da ke nuna za ta iya sauya sakamakon ba, amma har yanzu akwai lokaci da za a shigar da kararraki.

Da zarar jihohin sun tabbatar da kuri’un, masu zabe da suka yi alkawari za su jefa kuri’unsu a kwalejin zabe a tsakiyar watan Disamba.

Daga nan sai ‘yan majalisa su tabbatar da sakamakon zaben kwalejin a farkon watan Janairu, kusan mako biyu kafin ranar bikin rantsarwa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG