Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Sanin Sakamakon Zabe Ya Sa Wasu Amurkawa Gudanar da Zanga Zanga


Masu zanga zanga sun fito a garuruwa da dama jiya Laraba don kiran da a kammala kirga kuri’un zaben shugaban Amurka.

Wasu rukuni ‘yan kadan masu goyon bayan Shugaba Trump sun taru a wajen cibiyoyin kidayar kuri’u da ke jihohin Michigan da Arizona.

Haka kuma masu zanga zanga sun yi tattaki a biranen Chicago, Los Angeles, Seattle, Houston, Pittsburgh, Minneapolis da kuma San Diego.

Baya ga kiran a kirga kuri’u, masu zanga zangar sun kuma nuna yadda ake nuna rashin daidaiton jinsi, da shine ya haddasa zanga zanga a duk fadin Amurka a wannan shekarar.

Magoya bayan Shugaban kasa Donald Trump sun je wurin kidayar kuri’u a garin Detroit na jihar Michigan, suna neman a dakatar da kidayar da ake yi. Wadanda suka yi nasu gangamin daga baya a garin Phoenix na jihar Arizona, suna rera cewa, “A dakatar da sata”.

Zanga zanga iri iri na faruwa ne sanadiyyar ci gaba da rashin sanin tabbas game da zaben da aka yi tun ranar Talata, da kuma ikirarin da Shugaban kasa ya yi ba tare da gabatar da hujja ba, cewa an yi magudin zabe yayin da kuma ‘yan Republican suka shigar da kararraki da yawa game da zaben.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG