Hukumar Lafiya Ta Duniya, wato WHO, ta ce mai yiwuwa matasa da mutane masu lafiya za su jira zuwa shekarar 2022 kafin ayi musu allurar rigakafin COVID-19. Dalilin haka shi ne aga cewa allurar ta wadaci masu tsananin bukatarta.
Ranar Litinin 12 ga watan Oktoba Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa soke rundinar ‘yan sanda ta musamman mai yaki da ‘yan fashi wato SARS shine mataki na farko na yin garambawul a tsarin aikin ‘yan sanda da gwamnatinsa ta yi.
Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar gyara dangantaka tsakanin kasar da Hadaddiyar Daular Larabawa da ake kira UAE a takaice.
Kwamitin shari'a na Majalisar Dattawan Amurka ya fara zaman tantance Amy Coney Barrett wadda Shugaba Donald Trump ya zaba ta zama mai shari'a a kotun kolin Amurka.
Masana kimiyya a Australia sun gano cewa kwayar cutar coronavirus da ke haifar da COVID-19 za ta iya jure rayuwa akan wasu abubuwa har zuwa tsawon kwanaki 28.
A safiyar ranar Litinin 12 ga watan Oktoba ne aka yi bukin bayar da tallafin kudaden kungiyar Tarayyar Turai ga wasu kungiyoyin cikin gida a Nijar masu ayyukan kyautata rayuwar al’uma.
Bisa ga dukan alamu dole Najeriya ta nemi agajin da zai ba ta sararin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2021 na Naira tiriliyan 13.08 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar wa hadaddiyar majalisar kasa.
Ganin yadda ake yawan samun ayyukan ta'addanci da kai hare-hare a wasu yankunan Najeriya ya sa cibiyar wanzar da zaman lafiya da ke Kaduna shirya wani taron kara wa juna sani na malaman addinai.
A yayin da aka cika shekaru 3 da rasuwar wasu sojojin Amurka 4 da na Nijar 4 sakamakon kwanton baunar da ya rutsa da su a ranar 4 ga watan okotoban shekarar 2017 a kauyen Tongo Tongo, Ofishin jakadancin Amurka a birnin Yamai ya shirya wani taron addu’o'i a domin tunawa da su.
Gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya ta dakatar da yajin aikin gamagari da ta fara da misalin karfe 12 na safiyar yau Litinin, wanda da aka tsara zai kai tsawon makonni biyu.
Kasar Somaliya mai fama da rigingimun siyasa da matsalolin tsaro, ta yi sabon Firaminista, wanda ake masa kallon sabon shiga a fagen siyasa, Mohamed Hussein Roble.
Masu ruwa da tsaki na ci gaba da kokarin inganta al'amura a kasar Mali tun bayan da aka yi juyin mulki. Na baya bayan nan shi ne kokarin kawar da takunkumi a kasar ta Mali.
A ci gaba da fadi tashin samo magungunan cutar corona a Amurka, wani sanannen kamfanin harhada magunguna ya yi shelar kai wa mataki na karshe na gwajin wani magani nasa.
A wani al'ami mai nuna alamar har yanzu da sauran rina a kaba game da rigimar shugabanci, siyasa da kuma matsalar tsaro, kasar ta ce ta kama wasu mutane 41 da dinbin abubuwan fashewa.
Sanadiyyar Dirowa da mahaukaciyar guguwar nan ta Sally ta yi a yankunan gabar teku musamman a jahar Alabama ta Amurka, mutane da dama sun rasa wutar lantarki baya ga wasu nau'ukan barna masu yawan gaske.
Domin Kari