Shugaban kasar Kyrgyzstan Sooranbi Jeenbekov ya yi murabus yau Alhamis bayan an shafe kwanaki 10 ana tashin hanakali biyo bayan takaddamar zabe, yana cewa yana son ya kau da arangama tsakani jami’an tsaro da masu zanga zanga wadanda suke neman ya sauka daga kan kujerarsa.
Kirgistan ta fada cikin rikici tun ranar zaben ‘yan majalisa na ranar 4 ga watan Oktoba, wanda ‘yan adawa suka yi watsi da shi bayan da aka bayyana abokanan Jeenbekov a matsayin wadanda suka lashe zaben.
Bayan da magoya bayan ‘yan adawa suka fantsama kan tituna da kuma kwace gine gine na gwamnati, hukumomi sun soke zaben. Jeenbekov ya sanar a makon da wuce cewa zai yi murabus. Amma a wannan makon ya dan jinkirta, yana cewa zai cigaba da zama a kujerarsa har sai an gudanar da sabon zabe.
A jiya Laraba, Jeenbekov ya amince da zabin majalisar na Sadyr Japarov, mai kishin kasa wanda magoya bayansa suka fito da shi daga gidan yari a makon da ya gabata, don ya zama firai minista. Japarov da magoya bayansa sun bukaci Jeenbekov ya sauka.
Facebook Forum