Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya ayyana dokar ta baci a kananan hukumomi uku da wasu garuruwa na jihar, bayan sake barkewar hare-haren ‘yan bindiga.
Jam’iyyar APC mai mulikin Najeriya ta sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC cewa Bashir Machina shine dan takararta na Sanatan Yobe ta Arewa, matakin da a karshe ya tabbatar da makomar takarar shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan.
Rahotanni sun nuna cewa a yanzu haka akwai daruruwan makarantun firamare da sakandire da ke rufe a sakamakon matsalar ‘yan bindiga masu satar mutane domin neman kudin fansa.
Kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN) ta bukaci gwamnatin Tarayya da ta dauki matakan gaggawa na sasanta rikicin da ke tsakanin kamfanin siminti na Dangote da ke Obajana da kuma gwamantin Kogi kan mallakar fili.
Wata Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta umarci kungiyar malaman jami’oi ta kasa a Najeriya (ASUU) da ta janye yajin aikin da ta ke yi cikin gaggawa.
Jami’an sojin kasar Burkina Faso sun ce an gudanar da juyin mulki da ya hambarar da gwamnatin mulkin sojin kasar.
Batun kiyaye laffuza da kalamai yayin tallar ‘yan takara na daga cikin muhimman abubuwan da suka mamaye jawaban shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yanci daga Turawan mulkin mallaka na kasar Burtaniya.
Mawaki Ice Prince ya shiga hannun jami'an tsaro da sanyin safiyar yau Jumma'a a jihar Legas akan yin tuki da lambar mota mara lasisi, da kuma yi wa jami'in dan sanda barazana.
Mako guda kafin wa’adin tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya kare a watan Janairun bara, ‘yan jam’iyyar Republican 10 a majalisar wakilai sun bi sahun gaba daya ‘yan Democrat wajen kada kuri’ar tsige shi saboda tada tarzoma da aka yi a ranar 6 ga watan Janairu a ginin majalisar dokokin Amurka.
Ma’aikatar lafiya ta ce barkewar cutar Kyanda ta kashe yara 80 a kasar Zimbabwe tun daga watan Afrilu, inda ta dora alhakin kan tarukan da coci-coci ke yi.
Domin Kari