Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Burkina Faso: Rashin Tsaro Ne Yasa Muka Hambarar Da Gwamnati


Kaftin Ibrahim Traore
Kaftin Ibrahim Traore

Jami’an sojin kasar Burkina Faso sun ce an gudanar da juyin mulki da ya hambarar da gwamnatin mulkin sojin kasar.

Shugaban rundunar sojin kasar, Ibrahim Traore, ya ba da sanarwa da yammacin ranar Jumma’a cewa, sojoji sun karbe mulki yayin da suka hambarar da shugaban kasar na mulkin soji, Paul Henri Damiba, wanda shi kan sa ya karbe mulkin ne a wani juyij mulki watanni 8 da suka gabata.

Traore ya fada a wata sanarwa cewa wani gungun jami’an sojin da suka taimaka wa Damiba ya karbe mulki a watan Janairun da ya gabata, sun yi matsayar cewa shugaban ba zai iya kawo gyara da tsaro a kasar ba, wadda ta dade tana fama da tashin hankalin addini.

Wani jami’in soji ne ya gabatar da sanarwar da Traore ya rattaba wa hannu a gidan talabijin da yammacin ranar Jumma’a.

Sanarwar ta Traore ta ci gaba da cewa “a yayin da muke fuskantar tabarbarewar al’amura, mun yi ta yunkuri a lokuta da dama domin nusar da Damiba da ya maida hankalin gwamnati kan yanayin tsaro.”

A lokacin da Damiba ya karbe mulki a watan Janairu da ya gabata bayan hambarar da shugaban kasa Roch Kabore, ya yi alkawarin samar da tsaro a kasar.

To sai dai kuma an ci gaba da tashin hankali a kasar, haka kuma rikicin siyasa ya kara ta’azzara a ‘yan watannin nan.

Juyin mulki ya auku ne jim kadan bayan dawowar Damiba daga babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ya gabatar da jawabi a birnin New York.

XS
SM
MD
LG