Fiye da shekara guda da rabi bayan haka, sannan kuma bayan kakkausar suka da aka yi ta yi wa ‘yan jam’iyyar Republican da suka fita karara suka yi adawa da shi, Trump ya dauki wani mataki na ramuwar gayya.
Hudu daga cikin ‘yan majalisar 10 da suka kada kuri’ar tsigewar sun zabi yin ritaya idan sun kammala wa’adinsu a watan Janairu mai zuwa, maimakon fuskantar ‘yan takarar da Trump ke marawa baya a zabukan fidda gwani na jam’iyyar.
Bugu da kari, wasu hudu sun sha kaye a rikicin cikin gida da Trump ya goyi bayan wadanda suke kalubalantarsu a cikin ‘yan watannin nan, don haka su ma za su bar majalisar.
Biyu ne daga cikin 10 kawai suka rage masu neman wani wa’adin shekaru biyu da za su shiga zaben watan Nuwamba, inda za su fafata da masu kalubalantarsu na Democrat.