Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Sassanta Gwamnatin Kogi Da Kamfanin Simintin Dangote - MAN


Shugaban MAN Inginiya Mansur Ahmed
Shugaban MAN Inginiya Mansur Ahmed

Kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN) ta bukaci gwamnatin Tarayya da ta dauki matakan gaggawa na sasanta rikicin da ke tsakanin kamfanin siminti na Dangote da ke Obajana da kuma gwamantin Kogi kan mallakar fili.

Inginiya Mansur Ahmed, Shugaban MAN, ya yi wannan kira ne yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin Lagos, game da taron shekara-shekara na kungiyar karo na 50 (AGM) mai taken “Ajandar bunkasa masana’antu a Najeriya na shekaru goma masu zuwa.”

Kamfanin dillanci labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa, a ranar Laraba ne wasu 'yan asalin wurin su ka rufe masana’antar simintin Dangote da ke Obajana bisa wasu dalilai da ake zargi da suka shafi yadda aka sayi kamfanin.

Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta bayar da umarnin rufe kamfanin bayan binciken da ta gudanar kan aikin masana’antar siminti da aka yi zargin cewa babu wani abinda ya nuna a hukamce cewa an sayi kamfanin.

Shugabannin gudanarwa na kamfanin simintin Dangote sun yi zargin cewa. an harbi ma’aikatan kamfanin akalla bakwai tare da raunata wasu da dama bayan da jami’an tsaron jihar sama da 500 dauke da makamai, da kungiyar ‘yan banga suka afkawa masana’anta simintin.

Ahmed ya bayyana ci gaban a matsayin “abun damuwa da kuma amfani da dabaru masu karfi da ba dole ba.”

A cewarsa, matakin da gwamnatin jihar ta dauka bai dace ba, kuma za’a iya magance shi yadda ya kamata, ta amfani da hanyoyin doka.

“Wannan lamarin abin damuwane sosai, da gwamnati za ta dauki mataki irin wannan na rufe masana’antar da ke samar da ayyukan yi da ayyukan tattalin arziki ga dimbin jama’ar jihar. Abin da ya dace a yi shi ne a kai kamfanin kotu, saboda wannan mataki haramtacce ne kuma ba zai faru a duk wani yanayi na tattalin arziki da aka saba gudanarwa ba. Muna fatan gwamnatin tarayya za ta sa baki domin kada a sake irin wannan lamari,”

Ahmed ya kuma bukaci gwamnati da ta sake duba matsayinta na kara haraji kan abin da ba barasa ba da kuma sauran abubuwan sha.

XS
SM
MD
LG