Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwayar Cutar COVID-19 Na Da Karfi Sosai - A Cewar Masana Kimiyya


Masanin kimiyya
Masanin kimiyya

Masana kimiyya a Australia sun gano cewa kwayar cutar coronavirus da ke haifar da COVID-19 za ta iya jure rayuwa akan wasu abubuwa har zuwa tsawon kwanaki 28. 

A wani bincike da aka wallafa ranar Litinin 12 ga watan Oktoba a wata mujallar kwayoyin cutar virus, masu bincike a cibiyar kimiyyar CSIRO ta Australia, sun gano cewa kwayar cutar SARS-COV-2 “ta na da karfi sosai,” ta na iya jure rayuwa akan wasu abubuawa a maki 20 na ma’aunin Celsius, idan aka kwatanta ta da kwayar cutar mura ta Flu, wacce ke kai tsawon kwanaki 17 a cikin wannan yanayin.

Masana kimiyya a cibiyar ta CSIRO sun kuma gano cewa ba za a iya kamuwa da kwayar cutar SARS-COV-2 ba bayan kusan sa’o’i 24 a maki 40 na ma'aunin Celsius.

Bayan haka, Masanan sun gano cewa sabuwar kwayar cutar ta coronavirus za ta iya jure rayuwa a kan abubuwa kamar kudin takarda, gilashi da ƙarfe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG