An jima ana mahawara akan wannan batu na sake tsayawa takarar tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan bayan da ya kara da Shugaba Buhari a shekarar 2015.
A kwanan nan ma magoya bayansa sun sake tayar da zancen a kafofin sada zumunta daban daban, har ma ake dangana jituwar da ke tsakanin Buhari da Jonathan din a wani shiri na sauyasheka domin Buhari ya mika wa Jonathan mulki a shekarar 2023 saboda ya gama wa'adinsa tun da dama a can baya shekara hudu yayi na cikakken wa'adi bayan ya tsaya takara a shekarar 2011, wani abu da Sanata Emmanuel Bwacha, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa,ya ce babu abin da zai hana Goodluck tsayawa takara idan Jam'iyarsa ta tsayar da shi.
Amma ga dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Katsina ta Arewa, Sanata Ahmed Babba Kaita, ba haka labarin yake ba. Ya ce doka ba ta ba shi izinin tsayawa ba, kuma tuni har an datse bakin tsanya a gyarar kundin tsarin mulki da aka yi a baya.
To saidai mai fashin baki a al'amuran yau da kullum, Abdulrahaman Buba Kwacham, ya ce ba daidai ba ne a ce Goodluck ya sake tsayawa takara a wanan kasa domin shi ne ya jagoranci lalacewar da kasa ta yi a lokacin da yayi mulkin kasar, Kwacham ya ce in har an tsayar da shi to 'yan Najeriya za su zama bayi nan gaba kadan.
A yanzu dai yan kasa sun zuba ido su ga yadda zata kaya a daidai lokacin da Majalisar Dokokin Kasa ke haramar yi wa kundin tsarin mulkin kasa kwaskwarima.
Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:
Facebook Forum