Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayyar Habasha Ta Zafafa Kai Farmakin Soja a Yankin Tigray


Fargabar yiwuwar barkewar yakin basasa na karuwa a kasar Habasha bayan da gwamnatin tarayyar kasar ta zafafa kai hare-hare a yankin Tigray.

Firai Ministan Habasha ya zafafa kai hare-hare ta sama a yankin Tigray da ke arewacin kasar a jiya Lahadi a zaman wani bangaren abinda ya kira "tabbatar da wanzuwar doka," lamarin da ke kara fargabar yiwuwar barkewar yakin basasa a kasar, wacce ita ce ta biyu a yawan jama'a a Afirka.

Firai Minista Abiy Ahmed ya bijire wa kiran da Majalisar Dinkin Duniya da kawayen kasar na yankin suka yi na hawa teburin sulhu da shugabannin yankin Tigray, garin kabilun da suka mamaye gwamnatin tarayya kafin ya hau mulki a shekarar 2018.

A makon da ya gabata ne Abiy ya kaddamar da farmakin sojan a lardin, ya na mai cewa dakaru masu biyayya ga shugabanni a can sun kai hari kan sansanin sojoji da kuma kokarin satar kayan aiki.

Ya kuma zargi shugabannin na Tigray da yin zagon kasa ga garambawul din da ya ke muradin yi wa dimokiradiyyar kasar.

Jiragen yakin gwamnati sun yi ta kai hare-hare a yankin wanda ke kan iyakar Sudan da Eritrea.

Ma’aikatan agaji a jiya Lahadi sun ba da rahoton an gwabza kazamin fada a yankuna da dama na yankin, inda suka ce akalla mutum shida suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata.

'Yan Tigray sun koka kan cewa Abiy wanda ya fito daga Oromo, kabila mafi girma a Habasha, ya na musu bi-ta-da-kulli a matsayin wani bangare na murkushe ayyukan take hakkin jama'a da cin hanci da rashawa da kasar ta fuskanta a baya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG