Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zaman Tantace Mai Shari'a Amy Coney Barret


Mai shari'a Amy Coney Barrett
Mai shari'a Amy Coney Barrett

Kwamitin shari'a na Majalisar Dattawan Amurka ya fara zaman tantance Amy Coney Barrett wadda Shugaba Donald Trump ya zaba ta zama mai shari'a a kotun kolin Amurka.

Amy Coney Barrett, da aka zaba ta zama mai shari’a a kotun kolin Amurka ta bayyana gaban sanatoci don zaman tabbatar da ita da aka fara ranar Litinin 12 ga watan Oktoba, inda za ta bayyana wa 'yan majalisar cewa "bai kamata kotuna su yi kokarin" yin manufofi ba, ya kamata su bar wannan aikin a hannun shugaban kasa da 'yan Majalisar dokoki.

A wata sanarwa da ta fitar gabanin zaman, Barrett ta bayyana fassarar aikin babbar kotun, ta na mai cewa "ba a tsara kotun ba ne don warware kowacce matsala ko kuma gyara abubuwan da ba daidai ba na rayuwar al’umma."

Maimakon haka, ta ce, “shawarwarin yin manufofi da hukunce-hukuncen gwamnati, dole ne bangaren gwamnati da jama’a suka zaba su yi su.

"Bai kamata jama'a su sa ran kotuna za su yi haka ba, kuma suma kotunan bai kamata su yi kokarin yin hakan ba," a cewarta.

Barret yar shekaru 48, mai ra'ayin mazan jiya, wadda ita ce ta uku da Shugaba Donald Trump ya zaba don zama mai shari’a a kotun kolin Amurka mai alkalai 9, za ta yi kwanaki 4 ta na bada bayani a gaban kwamitin shari’a na Majalisar Dattawa a wannan makon.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG